Kotu ta raba auren Sadia da mijinta a kan batan dan diras

Kotu ta raba auren Sadia da mijinta a kan batan dan diras

A ranar Laraba ne wata kotun gargajiya da ke zamanta a yankin Mapo a garin Ibadan ta raba auren wata mata da mijinta a kan batan dan kamfai.

Matar, mai suna Sadia Abbas, ta shigar da karar mijinta, Azeez, a kan batan dan kamfenta.

Sadia ta nemi kotu ta raba aurenta da Azeez bisa zargin cewa ya na shirin yin amfani da ita domin tsafi.

Ta sanar da alkalin kotun, Ademola Odunade, cewa rayuwarta tana cikin hatsari matukar ta cigaba da zama da Azeez.

Ta kara da cewa tun bayan aurenta da Azeez rayuwarta ta shiga cikin kunci.

"Bayan al'amura sun tsananta ne sai na fahimci cewa dan kamfena ya bata. Na duba ko ina ban ganshi ba, amma duk da haka ya ce min bai san inda ya ke ba.

"Amma abin mamaki sai ga dan kamfen ya bayyana bayan kwana biyu, an ajiyeshi a wurin da ina da tabbacin cewa na duba da farko ba ya nan.

"Allah ne kadai ya san mugun nufin da ke cikin zuciyarsa a kaina, saboda na sanar da shi cewa zamana da shi ya kare."

"Tun bayan aurenmu ya daina kulawa da ni, Kuma a hakan ya ke zuwa domin kwanciya da ni idan dare ya yi, idan kuma na ki amincewa ya tilasta min.

"Ya gaza nuna min kulawa hatta a lokacin da na ke dauke da juna biyu, amma a haka ya ke sa min ido duk inda na shiga," a cewar Sadia.

Kotu ta raba auren Sadia da mijinta a kan batan dan diras
Kotu ta raba auren Sadia da mijinta a kan batan dan diras
Asali: Depositphotos

A nasa bangaren, Azee ya musanta dukkan zargin da Sadia ke yi masa.

Azeez ya zargi Sadia da saka shi a cikin cakwakiyar bashi har ta kai ga ya rasa jarin kasuwancinsa.

DUBA WANNAN: Bayan shekaru 22; Kifin da daliban jami'a ke neman sa'ar jarrabawa a wurinsa ya mutu

DUBA WANNAN: Yadda muka kashe gagararren dan ta'adda, Terwase Gana - Rundunar soji

"Duk kudina na kasuwanci a hannunta ya lalace, ga ta da yawan mita da korafi.

"Ba ta dawowa gida sai tsakar dare har hakan ta fara taba rayuwar yaron da mu ka haifa."

"Yawancin lokuta a waje nake sayen abinci saboda ba ta son yi mana girki kuma da zarar mun samu sabani sai ta hada kayanta ba bar gida, ba zan kara ganinta ba sai bayan kwana biyu," a cewar Azeez.

A hukuncin da ya yanke, Odunade ya raba auren bisa hujjar cewa babu sauran soyayya a tsakanin Sadia da Azeez.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel