'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda a Imo, sun kwashi bindigu

'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda a Imo, sun kwashi bindigu

Wasu 'yan bindiga da ake zargin cewa 'yan fashi ne sun kai hari ofisoshin rundunar 'yan sanda a Egbu da ke Owerri da kuma Nkworji da ke yankin karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo.

'Yan bindigar da suka kai hari ofishin 'yan sanda na Nkwerre ranar Litinin, sun yanki wani dan sanda da wuka sannan sun kwace bindigarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun cinnawa motar 'yan sanda wuta kafin su bar ofishin 'yan sandan.

Wata majiya ta bayyana cewa dan sandan da aka garzaya da shi zuwa asibiti sakamakon raunin da ya samu ya mutu ranar Talata.

Majiyar ta bayyana cewa; "wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan fashi ne sun kaiwa 'yan sanda hari a Owerre Nkworji.

"Sun cinnawa motar 'yan sanda wuta sannan sun raunata dan sanda guda ta hanyar caccaka masa wuka.

"An garzaya da shi zuwa asibitin garin Orlu a ranar Litinim din amma kuma ya mutu ranar Talata," a cewar majiyar.

'Yan bindiga sun kai hari ofishin 'yan sanda a Imo, sun kwashi bindigu
Babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya
Asali: UGC

Kazalika, wasu 'yan bindigar sun kai wani harin daban a ofishin 'yan sanda na Egbu da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

KARANTA: Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, bidiyon yadda suke aiki

KARANTA: Yahoo-yahoo: An kama 'yan Najeriya hudu da laifin damfarar Banki a kasar waje

Wani shaidar gani da ido ya ce 'yan bindigar da suka kai hari ofishin 'yan sandan sun kwace bindigar dan sanda daya bayan sun raunta shi ta hanyar caccaka ma sa wuka a wani salo irin na 'yan bindigar farko.

Yayin da aka tuntubeshi, kwamishinan 'yan sandan jihar Imo, Isaac Akinmoyed, ya tabbatar da cewa an kaiwa mutanensa hari.

Duk ya tabbatar da cewa 'yan bindigar sun kwace bindigu, kwamishinan ya musanta rahoton cewa an kashe jami'in dan sanda sakamakon kai harin.

Da safiyar yau, Laraba, ne rundunar sojin Nigeria da ke atisayen AYEM APKATUMA III ta bayyana yadda ta kashe gagararren dan ta'addan Benue, Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana.

Kwamandan rundunar atisayen, Manjo Janar Moundhey Gadzama Ali ya bayyana hakan a daren ranar Talata a karamar hukumar Doma, jihar Nasarawa.

A karamar hukumar ne shelkwatar rundunar soji na musamman guda hudu su ke, kuma a nan ne kwamandan rundunar ya yi holen gawar dan ta'addan Gana.

Manjo Janar Gadzama Ali ya ce: "Na gayya ce ku a daren yau ne domin ku ganewa idanuwanku nasarar da dakarunmu na atisayen AYEM APKATUMA III suka samu.

"Da misalin karfe 12 na ranar Talata, muka samu bayanan sirri na motsin dan ta'addan mai suna Terwase Akwaza Agbadu, da akafi sani da Gana, akan titin Gbese-Gboko-Makurdi.

"Cikin kwanton bauna dakarun atisayen AYEM APKATUMA III suka ajiye shinge tsaro a titin da misalin karfe 1 na rana, inda suka yi musayar wuta da tawagar dan ta'addan AKA Gana.

"A musayar wutar ne aka kashe shi. A binciken wajen, an gano wadannan makaman; AK 47 guda 5, harsashin FN guda 1, bindigar fistol Beretta guda 2, bindigar PAG guda 3 da sauransu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng