Yafewa masu laifi: Gwamnan Bauchi ya gane kuskuren sa, ya roki afuwa

Yafewa masu laifi: Gwamnan Bauchi ya gane kuskuren sa, ya roki afuwa

- Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayar da hakuri a kan afuwa da ya yi wa wani kasurgumin mai lalata bisa rashin sani

- An yi wa mai lalatan wanda ya kasance tsohon bursuna afuwa tare da wasu masu laifi a lokacin kullen korona

- Muhammed ya bayar da hakurin ne lokacin da kwamitin yaki da cin zarafin jinsi a jihar (SGBV) suka kai masa ziyara

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayar da hakuri a kan afuwa da yayi wa wani kasurgumin mai lalata bisa rashin sani.

An yi wa tsohon fursunan afuwa tare da sauran masu laifi a lokacin kullen korona, The Guardian ta ruwaito.

Muhammed ya bayar da hakurin ne a ranar Talata, 8 ga watan Satumba, lokacin da kwamitin yaki da cin zarafin jinsi ta jihar (SGBV) ya kai masa ziyara.

KU KARANTA KUMA: 2023: Kusoshin APC guda 3 sun shirya kwace Adamawa daga hannun PDP

Yafewa masu laifi: Gwamnan Bauchi ya gane kuskuren sa, ya roki afuwa
Yafewa masu laifi: Gwamnan Bauchi ya gane kuskuren sa, ya roki afuwa Hoto: The Guardian
Source: UGC

Gwamnan ya bayyana cewa da a ce ya san tsohon bursunan mai lalata mutane ne da ba zai taba yarda ayi masa afuwa ba.

A Bauchi, abun bakin ciki ne, bayan dan wani lokaci ta ma’aikatar shari’a na fahimci cewa mun yi wa wasu kasurman masu fyade afuwa, mun yi wa matanmu laifi. Ba son ranmu bane aikata hakan,” in ji shi.

Mohammed ya ce cin zarafin jinsi ya zama wata annoba sannan ya yi alkawarin daukar tsatsauran mataki kan masu aikata hakan.

KU KARANTA KUMA: Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki

A wani labarin kuma, an shigar da karar kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Kogi, Abdulmumuni Danga, a gaban wata kotun Abuja bisa tuhuramsa da aikata fyade.

Hukumar 'yan sanda ce ta gurfanar da Danga a gaban kotu bisa zarginsa da aikata fyade da cin zalin wata mata mai suna Elizabeth Oyeniyi, wacce ke zaune a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Rundunar 'yan sanda tana tuhumar Danga da aikata laifuka guda 7 wadanda suka hada da fyade da cin zali, an shigar da karar ne a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja.

A jikin takardar shigar da kara mai dauke da sa hannun ACP Effiong Asuquo, rundunar 'yan sanda ta ce ta gurfanar da Danga ne amadadin gwamnatin tarayya.

An shigar da karar Danga tare da wani mutum guda mai suna Success Omadivi, mai shekaru 35 a duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel