Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki

Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki

Gwamna Godwin Obaseki ya bayyana cewa zai dauki kaddara idan har ya sha kaye a zabe na gaskiya da adalci.

Obaseki ya bayyana hakan ne a yayinda ya zanta da manema labarai bayan ya ziyarci sufeto janar na yan sanda, Mohammed Adamu a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Ya ce a matsayinsa na dan damokradiyya, zai karbi sakamakon zabe na gaskiya, inda ya kara da cewa: “amma daga dukkanin alamu a yau, ina da tabbacin yin nasara.”

Sai dai kuma ya nuna damuwa game da tsaron masu zabe a jihar Edo.

KU KARANTA KUMA: 2023: Kusoshin APC guda 3 sun shirya kwace Adamawa daga hannun PDP

Ya ce ya ziyarci IGP ne saboda ya damu da lamarin tsaro.

Dan takarar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa sun kammala kamfen a unguwanni 192 na jihar Edo kuma cewa babban damuwarsu shine game da rikici a lokacin zaben.

Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki
Zan dauki kaddara idan na sha kaye a zabe na gaskiya - Obaseki Hoto: Vanguard
Source: Depositphotos

Ya ce akwai fargaba a jihar biyo bayan rikice-rikice da aka samu a jihar a makon da ya gabata.

Obaseki ya ce sun tattara irin wannan lamari na rikici 10 sannan sun gabatar da su ga IGP domin daukar mataki.

Ya ce hare-haren sun kasance a kan mambobin jam’iyyarsa kuma kaso 80 na hare-haren ya wakana ne a Edo ta arewa.

Gwamnan ya yi korafin cewa sun kai rahoton lamuran ga yan sanda, amma babu wanda aka kama.

Ya yi roko cewa ya kamata ayi wani abu game da lamuran.

Obaseki ya ce PDP ta jajirce domin tabbatar da cewar an samu zaman lafiya a lokacin zaben.

Ya bukaci rundunar yan sandan da ta sanar da kowa cewa ba za a nuna son kai ba, sannan cewa za a yi zabe na gaskiya cikin lumana.

KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen mutane 18 da suka shiga sahun masu kudin duniya a 2020

IGP Adamu ya ce rundunar yan sandan ba za ta lamunci tashin hankali daga kowa ba.

Ya bukaci jam’iyyun da su fadawa mambobinsu cewa su guji tada rikici.

A wani labarin, mun ji cewa a yayinda da zaben gwamnan jihar Edo ke kara gabatowa, alamu sun nuna cewa Gwamna Godwin Obaseki ya fara rasa wasu magoya bayansa a jam'iyyar PDP.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel