Karin farashin man fetur: Jama'ar Kaduna sun koka da ninkuwar kudin mota

Karin farashin man fetur: Jama'ar Kaduna sun koka da ninkuwar kudin mota

Masu kaiwa da kawowa a motocin haya a birnin Kaduna sun koka da yadda masu motocin haya suka ninka kudin mota sakamakon karin farashin litar man fetur.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, a ranar Laraba jama'a sun bayyana yadda suka dinga biyan kudin mota ninki a birnin Kaduna saboda karin farashin man fetur.

Gwamnatin tarayya ta daga farashin litar man fetur daga N145 zuwa N151.56 a makon da ya gabata.

Grace Musa da ke yankin Sabo, ta sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa, a yanzu tana biyan N200 a maimakon N100 daga Sabo zuwa Kasuwa.

Ta kara da cewa, tana kashe a kalla N500 a kowacce rana na kudin mota daga gidanta zuwa da dowawa wurin aikinta.

"Muna cikin matsanancin hali a yanzu wanda da kyar muke iya kula da iyalanmu," ta jajanta.

Silas Bawa kuwa mazaunin Narayi ne, wanda yace yana kashe N600 a kowacce rana a maimakon N200 da yake kashewa a da.

KU KARANTA: Yadda jami'ai suka yi wa matashiya fyade a motar kaita asbiti bayan kamuwa da korona

Karin farashin man fetur: Jama'ar Kaduna sun koka da ninkuwar kudin mota
Karin farashin man fetur: Jama'ar Kaduna sun koka da ninkuwar kudin mota. Hoto daga Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 14 a Zamfara, ta kwashe gada a Sokoto

"Idan wannan halin da muke ciki ya cigaba, babu shakka da yawanmu zamu koma tafiya a kasa.

"A da ina biyan N200 daga Narayi zuwa kasuwa baya da kudin babur da nake biya zuwa ofishina tunda an hana adaidaita sahu hawa manyan titunanmu," yace.

Mallam Garba Mohammed, direban motar haya ne wanda ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa dole ce ta sa suka kara kudin mota.

"A halin yanzu muna siyan litar man fetur a N161 a maimakon N148 da muke siya a da. Dole ce ta sa direbobi suka kara kudin mota," yace.

Aliyu Maikano wani direba ne wanda ke zama a Kurmin mashi. Ya ce tun bayan da aka kara farashin litar man fetur suke kira ga gwamnati da ta duba jama'a talakawa ta rage.

Amma kuma, PPRA, hukumar gwamnatin tarayya da ke da alhakin kayyade farashin albarkatun man fetur, ta ce daga yanzu babu ruwanta da maganar tsayar da farashin mai, magana ta koma hannun 'yan kasuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa babban sakataren hukumar PPRA, Abdulkadir Saidu, ne ya sanar da hakan. A cewar jaridar Punch, Saidu ya bayyana cewa daga yanzu kayyade farashin litar mai zai dogara ne a kan bukatarsa da kuma farashin danyen mai a kauwar duniya.

Hakan na nufin gwamnati ta tsame hannunta daga tsayarwa ko kayyade farashin litar mai. Saidu, wanda babban manaja a PPRA, Victor Shidok, ya wakilta, ya ce PPRA za ta cigaba da sa-ido a kan yadda 'yan kasuwa ke sayar da man fetur domin tabbatar da cewa ba a zalunci jama'a ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel