Jerin sunayen mutane 18 da suka shiga sahun masu kudin duniya a 2020

Jerin sunayen mutane 18 da suka shiga sahun masu kudin duniya a 2020

- Sabbin biloniya goma sha takwas sun samu shiga cikin jerin masu kudi 400 na duniya wanda mujallar Forbes ta wallafa

- Mafi akasarin sabbin masu kudin sun samu kudadensu ne daga mallakar hannayen jari

- Eric Yuan, shugaban kamfanin Zoom, shine a saman sabbin shigan da kudi da ya kai kimanin $11 biliyan

Duk da annobar korona, akwai mutanen da ke samun tarin arziki. Jerin biloniya 400 da mujallar Forbes ta saki ya tabbatar da hakan domin an samu karin sabbin masu kudi 18 a ciki.

A cewar mujallar Forbes, kadarorin da wadannan sabbin attajiran suka mallaka sun hada da mallakar kafar sadarwa da tattaunawa kai tsaye ta hanyar bidiyo a yanar gizo (Zoom), mallakar hannayen jari da kuma mallakar motocin da ke amfani da wutar lantarki.

A lura cewa sai mutum na da akalla $2.1 biliyan kafin ya samu shiga wannan jeri na masu kudi, ma’ana shine mafi karancin kudi na sabbin shigan.

Mujallar ta kuma bayyana cewa wasun su masu kudi ne dama sannan cewa barkewar annobar korona ta taimaka wa mutane.

Mutanen da suka ci moriyar annobar sune; Eric Yuan, Shugaban kafar sadarwa ta Zoom, da Alice Schwartz, wanda kamfaninsa ta Bio-Rad ta samar da kayayyakin gwajin korona.

An kuma samu biloniya daga bangaren samar da kayayyakin abinci.

Sheldon Lavin ya kasance Shugaban gidauniyar OSI, daya daga cikin manyan masu samar da abinci a duniya. McDonald ya kasance daya daga cikin abokan kasuwancinsa.

A shekarar dai, Trevor Milton, Shugaban kamfanin manyan motocin daukar kaya masu lantarki Nikola, dukiyarsa ta karu zuwa $3.3 biliyan.

Ya kuma kasance mafi karancin shekaru cikin sabbin shigan, yana da shekaru 38.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Obaseki na kara shiga matsala yayinda jiga-jigan PDP ke komawa APC

Jerin sunayen mutane 18 da suka shiga sahun masu kudin duniya a 2020

Jerin sunayen mutane 18 da suka shiga sahun masu kudin duniya a 2020 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ga jerin sunayen sabbin biloniyan su 18, kamfanoninsu, da yawan kudinsu a kasa:

1. Eric Yuan & family ($11 billion)

2. Sami Mnaymneh ($4 billion)

3.Tony Tamer ($4 billion)

4. Trevor Milton ($3.3 billion)

5. Ken Xie ($3.3 billion)

6. Barry Sternlicht ($3.2 billion)

7. Steven Klinsky ($3.1 billion)

8. Sheldon Lavin ($3 billion)

9. Pablo Legorreta ($2.8 billion)

10. Todd Wanek ($2.8 billion)

11. Jeff Green ($2.6 billion)

12. Jim Koch ($2.6 billion)

13. Rodney Sacks ($2.5 billion)

14. Valentin Gapontsev & family ($2.3 billion)

15. Jim McKelvey ($2.2 billion)

16. Alice Schwartz ($2.2 billion)

17. José E. Feliciano ($2.1 billion)

18. William Stone ($2.1 billion)

A wani labarin a baya chan mun ji cewa, Forbes ta ce ta cire sunayen attajiran kasar Saudiya dage jerin masu kudi na duniya sakamakon dabdalar zargin na rashawa.

Mujallar ta bayyana cewa, ta cire sunayen hamshakan 'yan Kasuwa na kasar Saudiya mai arzikin man fetur a sakamakon gwamnatin kasar da take zargin su da aikata laifuka na rashawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel