Zaben cike gurbi: PDP da APC za su ja daga a Bayelsa, Imo, Filato, da Legas

Zaben cike gurbi: PDP da APC za su ja daga a Bayelsa, Imo, Filato, da Legas

- Tsakanin karshen bara zuwa bana an rasa ‘Yan Majalisar dattawa shida

- Hukumar INEC za ta shirya zaben maye guraben Sanatocin 30 ga Oktoba

- PDP da kuma APC ne wadanda ake hangen za su fafata wajen lashe zaben

Yayin da ake shiryawa zabukan cike gurabe da za a yi a karshen watan Oktoban gobe, jaridar Daily Trust ta duba yadda jam’iyyun PDP da APC su ke shirin karawa.

APC da PDP su na da kujeru 59 da 43 yanzu haka a majalisar dattawa. Tilon jam’iyyar da ta ke da wakilcin sanata ita ce jam’iyyar YPP da ta iya cin zabe a Anambra.

Akwai kujeru shida daga jihohi biyar a majalisar dattawan kasar nan da hukumar INEC za ta gudanar da zaben cike gurbi domin samun sababbin wakilai a majalisa.

KU KARANTA: Mun shirya sulhu amma sai dai ... Tsohon Gwamnan APC

Wadannan kujeru su ne na mazabar Bayelsa ta tsakiya, Bayelsa ta yamma, Kuros Riba ta Arewa, Imo ta Arewa, Legas ta Gabas, da kuma shiyyar jihar Filato ta Kudu.

A jihar Bayelsa, Sanatocin sun yi nasarar lashe kujerun gwamna, a sauran jihohin hudu kuwa, ‘yan majalisar da su ke wakiltar mazabun sun mutu ne bayan an rantsar da su.

A ranar 8 ga watan Satumba aka kammala zabukan fitar da gwani, don haka kowace jam’iyya ta san ‘dan takarar da zai rike mata tuta a babban zaben da za ayi a Oktoba.

Tsohon gwamna Henry Seriake Dickson shi ne zai tsayawa PDP a matsayin ‘dan takarar Sanatan Bayelsa ta yamma, zai gwabza da Honarabul Peremowei Ebebi na APC.

KU KARANTA: Buhari ya sake fadawa Ministoci su je ofishin COS idan su na neman sa

Zaben cike gurbi: PDP da APC za su ja daga a Bayelsa, Imo, Filato, da Legas
APC da PDP su ne masu rike da kusan duka kujerun majalisa Hoto: Twitter/NgrSenate
Source: Facebook

A Bayelsa ta tsakiya kuwa, jam’iyyar APC ta tsaida Abel Ebifemowei ne a matsayin ‘dan takara, a gefe guda PDP mai mulki ta ba Moses Cleopas tikiti a zaben 31 ga Oktoba.

Sai kuma Legas inda mutanen gabashin jihar su ka rasa Sanata Bayo Osinowo. A nan, Tunde Gbadamosi da Tokunbo Abiru ne za su jarraba sa’ar zuwa majalisar tarayya.

Bayan mutuwar Sanata Ben Uwajumogu, APC ta zabi Frank Ibezim domin ya maye gurbinsa, ita kuma jam’iyyar PDP ta na shirin ganin Ifeanyi Ararume ya koma majalisa.

A kudancin Filato, jam’iyyar APC ta ba Farfesa Nora Ladi Dadu’ut tuta, wannan malamar makaranta za ta hadu ne da babban ‘dan siyasar nan, George Edward Daika.

Dazu kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala James Ngilari ya sauya sheka zuwa APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel