Zaben Edo: Obaseki na kara shiga matsala yayinda jiga-jigan PDP ke komawa APC

Zaben Edo: Obaseki na kara shiga matsala yayinda jiga-jigan PDP ke komawa APC

- Ga dukkan alamu Gwamna Godwin Obaseki na fuskantar tawaye gabannin zaben gwamnan jihar Edo

- Hakan ya kasance ne yayinda PDP a jihar ta rasa wasu manyan mambobinta ga APC a ranar Talata, 8 ga watan Satumba

- Daya daga cikin wadannan jiga-jigai shine tsohon mamba na majalisar dokokin jihar, Paul Odaro

A yayinda da zaben gwamnan jihar Edo ke kara gabatowa, alamu sun nuna cewa Gwamna Godwin Obaseki ya fara rasa wasu magoya bayansa a jam'iyyar PDP.

A ranar Talata ne wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Edo, Mista Paul Odaro, ya jagoranci masu sauya sheka daga jam'iyyar a karamar hukumar Uhunmwonde da ke jihar, zuwa APC, PM News ta ruwaito.

A gangamin APC na unguwa-unguwa a Egyaholir, Odaro ya ce rashin cika alkawaran zaben da Gwamna Godwin Obaseki ya dauka ne ya sa suka sauya sheka.

Zaben Edo: Obaseki na kara shiga matsala yayinda jiga-jigan PDP ke komawa APC
Zaben Edo: Obaseki na kara shiga matsala yayinda jiga-jigan PDP ke komawa APC Hoto: www.vangardngr.com
Source: Depositphotos

Ya ce ya kasance dan PDP tun 1999 amma ya yanke shawarar sauya sheka saboda yasar da unguwarsa da gwamnatin Obaseki tayi.

KU KARANTA KUMA: Karin farashin man fetur: Yan sanda sun ce ba za su bari ayi zanga-zanga ba a jihar Borno

Odaro ya ce koda dai Obaseki ya fito daga yankinsa, ya ce gwamnan bai aiwatar da kowani aiki a wajen ba.

Kwamrad Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar ya koka a kan watsi da ayyukan ci gaba da ya ce gwamnatin Obaseki tayi a yankin.

Oshiomhole ya bayyana cewa abun damuwa ne ganin cewa hatta da ginin ruwa da ke gaban fadar sarki gwamnan ya kasa bashi kulawa.

Ya ce abun damuwa ne cewa gwamnan na rufe makarantun jami’a da kuma kin daukar malamai a makarantun gwamnati, yana hana mutane samun ilimi mai inganci.

Saboda haka, Oshiomhole ya bukaci jama’a a yankin da su zabi APC a zaben ranar 19 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan

A gefe guda, Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo, ya ce zai binne Adams Oshiomhole, tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a siyasance a zabe mai zuwa.

Da yake magana a lokacin kamfen din jam’iyyar PDP a karamar hukumar Oredo da ke jihar, Obaseki ya ce zaben ranar 19 ya watan Satumba zai kasance takara da Oshiomhole.

Gwamnan wanda ya kasance dan takarar PDP a zaben, ya ce Oshiomhole, wanda ya sauka daga kujerar shugabancin jihar kafin ya hau, zai dandana kudarsa a zaben saboda baya ganin mutuncin mutanen jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel