Atiku: Idan har da gaske an bar ‘Yan kasuwa su tsaida farashin mai, araha zai yi

Atiku: Idan har da gaske an bar ‘Yan kasuwa su tsaida farashin mai, araha zai yi

Atiku Abubakar wanda ya yi alkawarin cire tallafin man fetur a lokacin da ya ke yakin neman zaben shugaban kasa ya gamu da suka a kan wannan zarafi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce akwai badakala da rashin gaskiya a yadda ake biyan ‘yan kasuwa tallafin mai, ya ce wannan ya hana kasar nan cigaba.

A farkon watan Satumban nan sai aka ji cewa humumar PPMC ta bayyana karin farashin man fetur, ta bada umarni a rika bada sarin lita a kan N138 zuwa N156.

Wannan canjin farashi da aka samu ya jawo ana saida man fetur tsakanin N159 da N162 a gidajen mai.

Alhaji Atiku Abubakar ya fito ya yi magana game da lamarin, ya ce ya kamata ace kudin fetur ya yi kasa idan aka yi la’akari da abin da ake saida gangar danyen mai.

KU KARANTA: Dr. Isa Pantami ya na kokawa da tashin farashin mai kafin zama Minista

Atiku ya yi jawabi a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ce kamata ya yi ace litar mai ta sauko ganin yadda kasuwar danye mai ta Duniya ta yi kasa a wannan shekara.

Mutane ba su bar jagoran adawar haka kawai ba, inda aka shiga maida masa martani a Twitter, fiye da mutane 2, 000 suka yi masa raddi, har da masu kausasan maganganu.

Atiku wanda sanannen ‘dan kasuwa ne ya jefawa gwamnatin tarayya tambaya a kan dalilin da ya sa fetur ya ke kara tsada, a lokacin da ya ke rage kudi a Amurka da Turai.

Atiku ya rubuta: “Ni ‘dan kasuwa ne. Ina kallon abubuwa ta madubin tattalin arziki. Tambayoyi na kishin amsoshi. Farashin danyen mai ya yi kasa daga inda ya ke a 2019.”

“A Amurka da Turai, farashin mai ya yi kasa sosai daga yadda su ke a shekarar 2019. Idan da gaske gwamnati ta cire hannunta, shin ba sauka farashi ya kamata ya yi ba?"

KU KARANTA: Har N600 an saida litar man fetur a lokacin PDP - Buhari

Ibrahim Ahmed Tijjani ya fadawa Atiku cewa ya kamata ace ya san Najeriya ta na wahalar samun kudin kasar waje don haka shigo da tataccen mai daga kasashen ketare ya ke tsada.

Wani kuma ya ce Atiku bai yi la’akari da karya darajar Naira da aka yi ba, wannan ya sa shigo da kaya daga waje ya ke da tsada. Ya ce bari ta nan, me ya hana matatun kasar aiki tun 1999?

Atiku: Idan har da gaske an bar ‘Yan kasuwa su tsaida farashin mai, araha zai yi
Atiku Abubakar Hoto: Medium
Source: UGC

Barin farashi a hannun ‘yan kasuwa bai nufin araha inji Bayo Adedosu. Wannan Bawan Allah ya ce: “Abin da hakan ke nufi shi ne farashi zai rika yawo a kullum, bisa la’akari da wasu abubuwa.”

A cewar Gbola Gbadamosi, abin da Atiku ya fada ba daidai bane. “Ka na da abokai a Amurka a Turai, ka sake tuntubar wasu daga cikinsu ka ji ko mai ya rage kudi a Turai. A ilmina, ba haka bane.”

A watan Yuni ne hukumar PPPRA ta dauki matakin barin farashin mai a hannun ‘yan kasuwa. Hakan ya sa gwamnati ta cire hannunta a harkar saida mai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel