Shehu Sani ya ce shigo da masara bayan rufe iyakoki kamar an yi-ba a yi ba ne

Shehu Sani ya ce shigo da masara bayan rufe iyakoki kamar an yi-ba a yi ba ne

- Gwamnatin Buhari ta haramta shigo da kayan abinci daga kasashen ketare

- Shugaban kasa ya bada umarnin a kawo masara bayan kudin abinci ya tashi

- Shehu Sani ya ce wannan umarni da aka bada ya ci karo da manufar Buhari

Ku na da labari cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta rufe iyakokin Najeriya, ta hana shigo da kaya daga kasashen ketare.

Muhammadu Buhari ya yi wannan ne da nufin kasar ta iya noma abin da za ta ci, wannan zai jawo aikin yi da kuma rage kashe kudin kasar wajen Najeriya.

Wasu su na sukar wannan zarafi na gwamnatin APC, musamman idan aka ga yadda kayan abinci su ka yi wani irin mummunan tashin da ba a taba gani ba.

Ganin yadda farashin kaya su ka tashi, shugaban kasa ya bada umarnin shigo da abinci daga wasu kasashe, wannan ya ci karo da akidarsa ta noma abinci a gida.

KU KARANTA: Sai da aka saida litar fetur a kan N600 a mulkin PDP - Buhari

Shehu Sani wanda ya taba wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya tofa albarkacin bakinsa a game da wannan mataki da aka dauka.

Sanata Shehu Sani ya na ganin rufe iyakokin kasar da aka yi da sunan bunkasa harkar noma da kuma bada damar shigo da abinci yanzu, ya zama tafka da warwara.

Shehu Sani ya ce shigo da masara bayan rufe iyakoki kamar an yi-ba a iya ba ne
Sanata Shehu Sani Hoto: This Day
Source: Facebook

‘Dan siyasar mai shekara 52 ya ce gwamnatin tarayya ta sabawa kanta da kanta, tun da har ta amincewa wa wasu shigowa da masara a karkashin babban banki.

Tsohon ‘dan majalisar ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 8 ga watan Satumba, 2020. Sani ya yi wannan magana ne da karfe 11:20 na dare.

KU KARANTA: Buhari ya yi karin haske game da karin kudin shan wuta da aka yi

Ga abin da ya ke cewa:

“A rufe iyakoki da sunan inganta noman cikin gida, sannan yanzu babban bankin Najeriya na CBN ya dawo ya na bada damar shigo da tona 260, 000 na masara, tafka da warwara ne.”

Gwamnatin tarayya ta bada damar a kawo masara daga waje ne a sakamakon tsadan da kayan gida su ka yi, Buhari ya ce hakan zai taimakawa masu hada abincin dabbobi.

A halin yanzu kun samu labari cewa farashin masara da shinkafa sun yi tsadar da wasu ba su iya sayensu. A wasu wuraren buhun shinkafar kasar waje ya kai N30, 0000.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel