Za'a yiwa daliban jihar Ogun karin aji kai tsaye ba tare da sun zana jarrabawa ba idan suka koma makaranta a ranar 21 ga watan Satumba - Dapo Abiodun
Gwamnatin jihar Ogun ta bayar da sanarwar cewa da zarar daliban firamare na jihar sun koma makaranta a ranar 21 ga watan Satumba za ta yi musu karin aji kai tsaye ba tare da rubuta jarrabawa ba
Gwamnatin jihar Ogun ta umarci makarantu a jihar da su bude a ranar 21 ga watan Satumba a zango na farko na shekarar 2020/2021.
Gwamnatin ta kara cewa hakan ya biyo bayan komawar da daliban ajin karshe na sakandare suka yi kwanan nan, wadanda a halin yanzu suke zana jarrabawar WAEC.
Kunle Somorin, wanda yake shine sakataren yada labarai na gwamnan jihar Dapo Abiodun, ya bayyana cewa wannan bude makarantu da za ayi za'a bude ga duka daliban firamare, sakandare, kwaleji, da kuma makarantun gaba da sakandare.
Haka kuma ya kara da cewa a kokarin da suke na cika sharudan bude makarantu a jihar, anyi gyare-gyare ga awannin da daliban za su dinga yi a makaranta kamar haka:
Daliban aji 1 zuwa 3 na firamare, za su dinga zuwa makaranta daga karfe 8 na safe su tashi karfe 11 na rana; daliban aji 4 zuwa 6 na firamare, za su dinga zuwa daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3 na yamma.
KU KARANTA: Bidiyo: Yaro mai shekaru 11 yayi ceton rai, ya tuka kakarsa a mota zuwa asibiti
Haka kuma daliban aji 1 zuwa aji 3 na makarantar sakandare za su dinga zuwa makaranta daga karfe 8 na safe zuwa karfe 11 na rana; daliban aji 4 zuwa aji 6 na sakandare, za su dinga zuwa makaranta daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3 na yamma.
Daliban da basu kai na firamare ba, wato yara daga shekara 3 zuwa 5 ba za su koma makaranta ba har zuwa lokacin da za a sake fitowa da wani sabon tsari gare su.
Haka kuma makarantun kudi suma ana bukatar suyi kokarin su bi dokokin da aka gindaya wajen bude makarantun.
KU KARANTA: Da sana'ar sayar da kifi nake daukar nauyin karatun 'ya'yana a jami'a
Makarantun gaba da sakandare suma an basu umarnin budewa a ranar 21 ga watan Satumba.
Gwamnatin jihar tuni ta bayyana cewa ta yiwa daliban firamare karin aji ba tare da rubuta jarrabawa ba, sannan kuma daliban aji 6 na firamare an basu damar shiga aji daya na sakandare a jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng