Ba zamu taba kyale mujallar da ta wallafa hoton Annabi Muhammad ba a kasar Faransa - Ayatollah Khamenei

Ba zamu taba kyale mujallar da ta wallafa hoton Annabi Muhammad ba a kasar Faransa - Ayatollah Khamenei

Shubaga Ayatullah Khamenie na kasar Iran, ya fito ya bayyana cewa ba za su taba kyale mujallar Charlie Hebdo da ta wallafa hoton Annabi Muhammad ba, inda ya ce hakan babban laifi ne da cin zarafi ga fiyayyen halittar

Shugaban kasar Iran, Ayatollah Ali Khamenie, ya tabbatar da wallafa hoton Annabi Muhammad (SAW), a wata mujalla ta kasar Faransa mai suna CHarlie Hebdo.

Charlie Hebdo ta sake wallafa hoton Annabi Muhammad da Musulunci, wanda yayi sanadiyyar kai wani mummunan hari ga wannan mujalla a shekarar 2015.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata 8 ga watan Satumba, Khamenie, ya ce, mujallar ta kasar Faransa ta aikata babban laifi ta hanyar zagin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Ba zamu taba kyale mujallar da ta wallafa hoton Annabi Muhammad ba a kasar Faransa - Ayatollah Khamenei
Ba zamu taba kyale mujallar da ta wallafa hoton Annabi Muhammad ba a kasar Faransa - Ayatollah Khamenei
Asali: Twitter

Haka kuma ya kara magana akan irin yadda kasashen Turai suka dauki karan tsana suka dorawa Musulunci da Musulmai.

Haka kuma ya bayyana maganar da wasu 'yan siyasa na kasar Faransa suka yi akan nuna halin ko in kula, kuma suka ki yin Allah wadai da wannan abu da mujallar tayi.

KU KARANTA: Kashe-kashe: CAN da shugabannin kudancin Kaduna sun ki halartar taron sasanci

Shugaban kasar ta Iran ya ce:

"Saboda tsananin tsana da aka dauka aka dorawa addinin Musulunci da kuma gwamnatoci masu girman kai sune babban dalilin da ya sanya ake samun matsalar nan a kowanne lokaci," cewar Ayatollah Khamenie.

Ya kara da cewa wannan zagi da aka yi zai iya zama kokari ne na dauke hankalin yankin Asia ta Yamma da kuma gwamnatocinsu akan shirin da kasar Amurka take yi akan yankin.

"Kasashen Musulmai, musamman ma yankin Asia ta Yamma, dole su lura da kyau akan matsalar dake tinkaro wannan yanki, kuma kada mu taba mantawa da munafurcin kasashen Yamma akan addinin Musulunci da Musulmai."

Duk da wannan maganganu da wannan hoto ya jawo a kasashen Musulmai, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, yaki fitowa ya kushe wannan gidan mujalla da suka sake wallafa wannan hoto.

KU KARANTA: Talauci da lalacewar tattalin arziki na karuwa a kowacce rana a Najeriya - Osinbajo

A cewar shi, mujallar ta Charlie Hebdo, ba ta karya kowacce irin doka ba wajen sake wallafa wannan hoto, don tunawa da ranar 2 ga watan Satumba akan mummunan harin da aka kaiwa ofishinta a shekarar 2015, da masu tsattsaurar akida suka kai.

Haka kuma Legit.ng ta kawo muku irin tataburzar da ake ta fama a jihar Kano, kan matashin saurayi Yahaya Sharif-Aminu da ya zagi Annabi Muhammad (SAW) a cikin wata waka da yayi da ta dinga yawo a manhajar WhatsApp.

Hakan ya biyo bayan kungiyoyin kare hakkin dan adam da suka fito suka kalubalanci wannan hukunci da kotun shari'ar Musuluncin ta yanke akan saurayin, inda a yanzu dai haka an bashi damar daukaka kara, kuma yau ne kwanaki 30 da aka diba masa za su kare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel