Mun shirya yin sulhu yanzu a jihar Zamfara amma akwai matsala guda - AbdulAziz Yari

Mun shirya yin sulhu yanzu a jihar Zamfara amma akwai matsala guda - AbdulAziz Yari

- AbdulAziz Yari ya bayyana cewa shirye yake da yayi sulhu da Sanata Kabir Marafa

- Ya zargi Marafa da tura yaransa cikin gwamnatin PDP

- Wannan shine matsala guda da za'a samu wajen sulhu, a cewarsa

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Abubakar Yari, ya bayyana cewa mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar sun shirya yin sulhun gaske yanzu bayan rikicin cikin gida tsakaninsa da Sanata Kabiru Marafa.

Bangaren Kabiru Marafa da na Yari sun kasance cikin bakin kiyayya tun gabanin zaben 2019.

Yari ya jagoranci tawagar mambobin jam'iyyar zuwa wajen shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar APC, Mai Mala Buni, a Sakatariyar jam'iyyar dake Abuja.

Ya bayyana dalilan da ya sa ake bukatar sulhu a jihar, kuma ya ce dukkan abokan hamayya su gabato da niyya mai kyau.

Amma Yari yace matsalan shine wasu daga cikin mabiya Sanata Kabiru Marafa tuni sun hada kai da gwamnatin Bello Matawalle na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A cewarsa: "Mun shirya sulhu da kowa amma matsalan shine ta yaya za kayi sulhu da wanda ke da mambobinsa cikin gwamnati. Yana da sakataren gwamnatin jiha, yana da kwamishana, yana da kowa a wajen."

"Amma idan kowa ya shiryawa sulhu zamu sani saboda mun dade cikin wannan harkar tun shekarar 1999 amma da ikon Allah muna hangen rana goben jam'iyyar nan da 2023."

Mun shirya yin sulhu yanzu a jihar Zamfara amma akwai matsala guda - AbdulAziz Yari
Mun shirya yin sulhu yanzu a jihar Zamfara amma akwai matsala guda - AbdulAziz Yari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Shahrarren dan bindigan da ya addabi jihar Benue, Gana, ya shiga hannu

Asali: Legit.ng

Online view pixel