An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan

An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan

Yan Najeriya da dama sun caccaki iyalan shugaban kasa a kan karya dokar babban bankin Najeriya (CBN) a wajen bikin Hanan Buhari, daya daga cikin yaran shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mutane da dama sun kuma yi wasti da take dokar bayar da tazara a tsakanin jama’a wanda hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayar don hana yaduwar cutar Coronavirus.

Hanan da Turad, dan tsohon dan majalisar dokokin tarayya, Mahmud Sani Sha’aban, sun yi aure a fadar shugaban kasa a ranar Juma’a da ya gabata.

Bikin ya samu manyan jami’an gwamnati da yan siyasa.

Hotuna da bidiyon bikin ciki harda wanda uwargidar shugaban kasar, Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram sun yi fice a karshen makon.

KU KARANTA KUMA: Saudiyya ta soke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Khashoggi

A wani bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa, an gano ma’auratan na rawa tare wadanda suka halarci bikin inda aka yi ta lika kudi.

An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan
An caccaki Buhari da iyalansa kan karya dokokin CBN da NCDC a bikin Hanan Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

An taru waje daya ba tare da barin tazara ba a cikin bidiyon sannan mafi yawan mutanen da ke wajen basu sanya takunkumin fuska ba.

Wannan ya haifar da cecekuce yayinda mutane da dama suka nuna rashin jin dadinsu a kan yadda manyan mutane da sauran da suka hallara suka take dokokin CBN da na NCDC.

Da dama sun yi kira ga a hukunta wadanda suka take dokar yayinda wasu suka ce da an sani an dage bikin saboda annobar korona da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Abunda doka ya ce:

Sashi na 21 na dokar CBN ya yi gargadi a kan wulakanta Naira.

Ya bayyana hukuncin cin tarar N50,000 ko kuma watanni shida a gidan yari ko kuma duk hukuncin biyu ga wanda ya aikata laifin.

Cikin wannan doka kuwa harda na yiwa mutane liki da Naira a wajen taro ko kuma cukukuye kudin.

Bankin ya sha daukar alwashin bi ta kan duk wani mutum ko kungiya da aka samu da aikata wannan laifi, jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Yan gida daya su 6 sun mutu bayan gini ya ruso masu a Kebbi

Game da annobar korona kuma, jami’an NCDC da sauran manyan gwamnati ciki harda shugaban kasar, sun sha yin gargadi a kan take matakan kare kai da hukumar ta fitar.

An hukunta mutane da dama da suka take ka’idar ciki harda shahararrun yan wasa ta hanyar aikin shara ko biyan tara.

A halin da ake ciki, mabiya shafukan sada zumunta ne ke Allah wadai da lamarin.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin Shugaban kasar, Garba Shehu bai amsa kiran waya da aka yi masa ba.

Hazalika ba a samu jin ta bakin kakakin CBN, Isaac Okoroafor ba.

A gefe guda, Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa kuma uwar amarya, Hanan Buhari, ta yi korafi da mai zanen barkwanci, Mustapha Bulama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel