Za a daina bayar da katin shaidar dan kasa, Pantami ya zo da sabon tsari

Za a daina bayar da katin shaidar dan kasa, Pantami ya zo da sabon tsari

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta sanar da kammala shirinta na mayar da hukumar bayar da shaidar katin dan kasa (NIMC) karkashin ma'aikatar sadarwa.

A makon jiya ne sanarwar hakan ta fito bayan amincewar majisar zartarwa ta tarayya (FEC).

Bayan hakan ne ministan sadarwa da sabon tattalin arziki, Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana bullo da wani sabon tsari.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin PRNigeria, Pantami ya bayyana cewa za a maye gurbin katin dan kasa da ake bayarwa da wasu lambobi na musamman.

Minsitan ya bayyana cewa lambar, wacce za a fara bayar wa nan gaba, za ta yi wa 'yan Najeriya amfani wajen cin moriyar aiyukan gwamnati.

Za a daina bayar da katin shaidar dan kasa, Pantami ya zo da tsabon tsari
Za a daina bayar da katin shaidar dan kasa, Pantami ya zo da tsabon tsari
Source: Facebook

"Cigaban da ya zo shine na bayar da lamba, ba katin shaida ba. Za a dora lambar kowa a kan babbar na'ura ta gwamnati daga nan Kuma a yi amfani da ita a kan duk wasu takardu ma su dauke da bayanan da suka shafi mutum.

DUBA WANNAN: Mun tsame hannunmu daga tsayar da farashin man fetur - Gwamnatin tarayya

DUBA WANNAN: Cigaba: Ganduje ya saka na'urorin sa-ido a manyan titunan Kano, kalli bidiyon yadda suke aiki

"Da lambar Za a yi amfani wajen Yi wa mutum fasfo, lasisin tuka mota, da sauran takardun da duk mutum zai nema daga gwamnati.

"Ta hanyar amfani da ita wannan lamba mutum zai iya gudanar da harkokinsa, ba lallai sai ya dinga yawo da Kati ba.

"Zamani ya sauya, an samu cigaba, amfani da kati zai zama zabin mutum, shine cigaban da ya zo a duniya, Kuma ba Za a bad Najeriya a baya ba," a cewar Pantami.

A cewar Pantami, gudunmar da bangaren fasahar sarrafa bayanai (ICT) ya bayar ga tattalin arzikin kasa ta karu a tsakiyar shekarar 2020.

wani labarin da Legit.ng ta wallafa, PPRA, hukumar gwamnatin tarayya da ke da alhakin kayyade farashin man fetur, ta ce daga yanzu babu ruwanta da maganar farashin mai, magana ta koma hannun 'yan kasuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa babban sakataren hukumar PPRA, Abdulkadir Saidu, ne ya sanar da hakan.

A cewar jaridar Punch, Saidu ya bayyana cewa daga yanzu kayyade farashin litar mai zai dogara ne a kan bukatarsa da kuma farashin danyen mai a kauwar duniya.

Hakan na nufin gwamnati ta tsame hannunta daga tsayarwa ko kayyade farashin litar mai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel