Bayelsa: Sufetan ‘Yan Sanda ya ki kawo Vijah Opuama gaban kotu a karo na uku
Wani Alkalin babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya sake bada umarni ga jami’an ‘yan sanda su kawo masa Vijah Opuama a gabansa.
Wannan ne karo na uku da kotu ta fadawa Sufetan ‘yan sandan Najeriya cewa ta na bukatar ganin ‘dan takarar gwamnan na jihar Bayelsa a gaban kuliya.
A ranar 7 ga watan Satumba, jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa Alkali ya fadawa shugaban ‘yan sanda cewa ya na da bukatar ganin Vijah Opuama a kotu.
Alkali ya bada wannan sabon umarni ne a ranar Litinin a sakamakon gazawar ‘yan sanda na bin umarnin da ya bada a baya na fito masa da Vijah Opuama.
Alkali mai shari’a Taiwo Taiwo ya taba bada irin wannan umarni a ranakun 3 ga watan Agusta da kuma 2 ga watan Satumba, amma ba a yi masa biyayya ba.
KU KARANTA: Za mu ba Bola Tinubu mamaki a zaben Ondo – Jam’iyyar PDP
Jami’an ‘yan sanda sun cafke wanda ake nema ne a watan Agusta. Tun wannan lokaci ya na hannun jami’an tsaron yayin da shi kuma ya kai su kara a kotu.
Alkalin ya ke cewa: “Kotu ta bada umarnin kawo mata wanda ya shigar da kara a gabanta. Dole ayi wa wannan doka biyayya.”
“Don haka ina bada umarnin a kawo mani wanda ake tuhuma a ranar Laraba, 9 ga watan Satumba, 2020.”
“Dole a kawo wanda ake kara ba tare da bada wani uzuri ba.” Inji Mai shari’a.
Alkalin ya kuma tsaida 9 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a saurari shari’ar bada belin Mista Opuama.
KU KARANTA: Ministan jiragen sama ya yi gwajin COVID-19 sau 10
Lauyan da ya tsayawa wanda aka tsare, T. O Amalaha, ya roki Alkali ya daga shari’ar zuwa 16 ga watan Satumba, a madadin 9 ga wata, amma Alkali ya ki yarda.
Alkalin ya bayyana cewa ba zai karawa ‘yan sanda wa’adin mako guda ba, ganin sun yi watsi da umarni biyu da kotu ta bada a baya.
Taiwo Taiwo ya ce idan ‘yan sanda su ka ki kawo wanda ake tsarewa, “Zan bukaci IGP ya zo kotu.”
“Menene wahalar kawo mutum gaban kotu?” Alkalin ya tambaya.
Opuama ya na cikin wadanda su ka tsaya takarar gwamna a Bayelsa, an tsare shi ne a lokacin da ake sauraron karar da ya shigar na korafin zaben 2019.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng