Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno

Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno

Mayaƙan kungiyar Boko Haram sun kashe farar hula 10 a wasu hare-haren da suka kai wasu ƙauyuka uku a Borno kamar yadda masu tsaro na ƙauyukan suka sanar a ranar Litinin.

Babakura Kolo, shugaban kungiyar masu yaƙi da ƴan ta'addan da gwamnati ke mara wa baya ya shaida wa AFP cewa ƴan ta'addan sun kai hare haren ne a ranar Lahadi.

Kolo ya ce sun kai hari a ƙauyen Kumari mai nisan kilomita 40 daga babban birnin jihar Maiduguri, inda suka kashe mutane huɗu da ke barci.

Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno
Boko Haram ta kashe mutum huɗu yayin da suke barci, ta ƙona wasu uku da ransu a Borno. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

Ƴan ta'addan ba su yi amfani da bindigu ba domin kada dakarun sojoji da ke kusa su ji ƙarar harbin bindigan inji wani mamban kungiyar tsaron mai suna Ibrahim Liman.

Yan ta'addan sun dade suna kai hare hare a garin da bindigu wasu lokutan kuma harin ƙunar bakin wake.

A wani wurin kuma, majiyoyi sun ruwaito cewa ƴan ta'addan sun ƙona wasu mutane uku da ransu har lahira kuma suka kashe wasu hudu a wani ƙauye da ke wajen Maiduguri duk dai a ranar Lahadi.

An kuma kashe wasu manoma biyu a lokacin da suke aiki a gonakin su yayin da aka sace wasu da dama a kusa da birnin ta Maiduguri.

KU KARANTA: Katsina: Ƴan banga sun fafata da ƴan bindiga, mutum biyu sun mutu

Boko Haram sun tsananta kai wa manoma hare hare a gonakin su a lokacin da manoman ke ƙoƙarin yin aikin damina kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Rikicin na ƴan ta'addan da ya fara tun a shekarar 2009 ya yi sanadin mutuwar mutane kimanin 36,000 yayin da kimanin miliyan biyu suka rasa muhallan su.

Hare-haren ya yaɗu zuwa kasashen Nijar, Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya wadda hakan yasa ƙasashen ta kafa rundunar sojojin haɗin gwiwa don yaƙi da ƴan ta'addan.

A wani rahoton daban, kun ji an kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne a lokacin da ƴan banga a ƙauyen Yantara da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina suka yi fito na fito da ƴan bindiga da suka kai hari ƙauyen ranar Talata.

Wani mutum mai suna Mamman Dahiru mai shekaru 30 a duniya shima ya rasa ransa sakamakon harin.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel