Saudiyya ta soke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Khashoggi

Saudiyya ta soke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Khashoggi

Wata kotun Saudiyya a ranar Litinin, ta soke hukuncin kisa da aka zartar kan wasu mutum biyar da suka kashe dan jarida Jamal Khashoggi, a cikin wani hukuncin karshe.

Sai dai wannan sabon hukunci ya fuskanci suka daga budurwarsa da wani kwararre a majalisar dinkin duniya inda suka bayyana shi a matsayin rashin adalci.

Bisa ga wani hukunci da aka yanke bayan yaran Khashoggi sun yi afuwa ga makasan, inda suka nemi a sassauta hukunci, an yanke wa masu laifin su takwas da ba a bayyana sunansu ba hukuncin zama a gidan yari na tsakanin shekaru bakwai da 20.

KU KARANTA KUMA: Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida

Hukuncin kotun ya nuna iko a kan kokarin Saudiyya na shata layi a kisan da aka yi a watan Oktoba 2018 yayinda masarautar ta nemi dawo da martabarta a idon duniya gabannin taron G20 da za a yi a watan Nuwamba a birnin Riyadh.

An kammala shari’ar sirri na mutum 11 da ake zargi a watan Disamba, inda aka yanke wa mutum biyar da ba a bayyana sunayensu ba hukuncin kisa.

Sannan aka yanke wa sauran mutum uku zaman gidan yari na shekaru 24 kan kisan.

KU KARANTA KUMA: Dangin miji sun fatattaki mata saboda ta nemi hakkin yarta mai shekaru 8 da aka yi wa fyade

Saudiyya ta soke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Khashoggi
Saudiyya ta soke hukuncin kisa kan wadanda suka kashe Khashoggi Hoto: Channels TV
Source: UGC

Amma yafiyar iyalansa ya sa an sassauta hukuncin a ranar Litinin, ciki harda soke hukuncin kisa da aka yanke wa mutum biyar din, Channels TV ta ruwaito.

“An yanke wa mutum biyar cikin masu laifin shekaru 20 a gidan yari... mutum daya hukuncin shekaru 10 sannan sauran mutum biyu shekaru bakwai,” in ji jawabin mahukunta kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ta fitar.

A baya dai mun ji cewa Yariman kasar Saudi Arabia ya ce alhakin kisan dan jarida Jamal Khashoggi da aka yi yana wuyansa domin abin ya faru ne karkashin mulkinsa.

Basaraken, Mohammed bin Salman, dai bai fito ya yi bayani ga jama'a ba akan kisan dan jaridar da aka yi a ofishin jakadancin Saudi da ke Istanbul.

CIA da wasu jami'an gwamnatin gamma sun ce shi ya bada umarni amma jami'an Saudi sun ce babu hannunsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel