Ana rade-radin Juventus ta na cinikin Luis Suarez da Kungiyar Barcelona

Ana rade-radin Juventus ta na cinikin Luis Suarez da Kungiyar Barcelona

‘Dan wasan gaban Barcelona, Luis Suarez ya na shirin barin kasar Sifen ya koma Italiya, inda ake sa ran cewa kungiyar Juventus za ta biya kudinsa.

Juventus ta na ciniki da Barcelona na ganin ta dauke ‘dan wasan mai shekaru 33. Idan har cefane ya fada, ‘dan kwallon na kasar Uruguay zai yi sallama da La-liga.

Goal.com ta ce Luis Suarez zai shiga ajin koyon darasin harshen Italiyanci domin ya samu damar karbar fasfon kasar da ake kyautata zaton zai koma taka leda.

Ana kishin-kishin din cewa har Juventus ta daddale magana da Luis Suarez a kan cewa za a rika biyansa €10 a kowace shekara, kusan Naira biliyan biyar kenan.

KU KARANTA: Messi ya na da 'yancin ya bar Barcelona - Ramos

Luis Suarez zai sa hannu a kwangilar shekaru uku da zakarun Seria A, muddin aka karkare ciniki tsakanin shugabannin kungiyoyin Juventus da na Barcelona.

Kwantiragin Suarez a Barcelona zai kare ne a shekarar da za a shiga. Yarjejeniyar za ta sabunta kanta muddin ‘dan kwallon ya buga 60% na wasannin kungiyar.

Sabon kocin da Barcelona ta dauko haya, Ronald Koeman ya nuna cewa sam ba zai tafi da Luis Suarez ba, don haka Tauraron ya ke neman inda zai koma wasa.

KU KARANTA: Mahaifin Messi ya yi magana game da tashin 'Dan sa daga Sifen

Ana rade-radin Juventus ta na cinikin Luis Suarez da Kungiyar Barcelona
Watakila Luis Suarez ya koma Kungiyar Juventus Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

Idan cinikin ya fada, Suarez zai zama ‘dan wasa na 13 da ya samu damar yin wasa da Taurarin da ake ji da su a zamanin yau, Lionel Messi da Cristiano Ronaldo.

A gefe guda kuma, Barcelona za ta yi kokarin sayen ‘dan wasan Inter Milan, Lautaro Martinez domin ya maye gurbin da Luiz Suarez zai bari a gaban kungiyar.

Suarez ya zo Barcelona ne daga kungiyar Liverpool a 2014. A zamansa na shekaru shida, ya ci kwallaye kusan 200 da La-liga hudu, ya buga wasanni 283.

Rahotanni sun ce a halin yanzu Suarez ya na wasa ne shi kadai. Idan za ku tuna a makon nan ne Lionel Messi ya dawo aiki bayan ya yi barazanar barin Barcelona.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel