Kudin wuta: Masu samun lantarki a kai-a kai kurum mu ka yi wa kari inji Lai

Kudin wuta: Masu samun lantarki a kai-a kai kurum mu ka yi wa kari inji Lai

A makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta bada sanarwar karin kudin shan wutar lantarki. Jama’a da-dama sun fito su na kuka da wannan kari da aka yi.

Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed ya fayyace yadda wannan kari ya ke, ya ce ba kowa ba ne zai rika biyan karin kudi domin ya sha wutar lantarki.

Alhaji Lai Mohammed ya ce wadanda su ke samun akalla sa’o’i 12 na hasken wuta a kullum ne kurum za su ga canjin farashi a kudin wutan da su ke sha ko su ke saye.

Da ministan ya ke magana game da wannan lamari a ranar Litinin, Lai Mohammed ya ce karin da hukumar NERC ta yi zai yi aiki ne a kan wadanda su ka fi samun wuta.

KU KARANTA: Bidiyon Pantami ya na kokawa da tashin farashin kudin mai

Ministan ya zanta da manema labarai a ranar 7 ga watan Satumba, 2020, inda ya yi karin bayani.

Lai ya ce gwamnati ta dade ta na daukar dawainiyar kudin wutar da ake sha, a sakamakon saidawa ‘yan kasuwa kamfanonin lantarkin kasar da aka yi a gwamnatin baya.

Mai girma ministan ya ce: “Domin a samu a cigaba da aiki, gwamnati ta kashe Naira tiriliyan 1.7 yanzu a kan wuta, musamman wajen toshe gibin da ake samu.”

Lai ya ce gwamnatin tarayya ba ta da kudin da za ta cigaba da kashewa domin biyewa harkar wuta. A cewarsa bai dace a ci bashi don kurum a biya kudin lantarki ba.

Kudin wuta: Masu samun lantarki a kai-a kai kurum mu ka yi wa kari inji Lai
Ministan yada labarai da al'adu Lai Mohammed Hoto: WestPostNigeria
Source: Twitter

KU KARANTA: Buhari zai fara taimakawa masu karamin karfi bayan karin kudin mai

“Masu samun wuta na kasa da sa’a 12, ba za su samu canjin kudi ba. Wadanan su ne sahun masu shan wutan lantarkin da su ka fi yawa.” Inji Ministan yada labaran kasar.

Da wannan mataki da gwamnati ta dauka, babu ruwan mafi yawan jama’a da wannan kari da aka yi. Canjin farashin zai fi tasiri ne a kan attajiran da su ke samun wuta kan kari.

Gwamnati za ta yi kokarin ganin an samu na’urar auna shan wuta a gidajen kasar. NERC za ta dage wajen daura wannan na’ura a gidaje fiye da miliyan biyar a Najeriya.

Ya ce da wannan aiki da za a yi, mutane 250, 000 za su samu aikin yi, sannan har mutane miliyan 25 za su amfana da tsarin, tare da tabbatar da cewa mutane sun samu wuta.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel