Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 10, sun yi garkuwa da manoma

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 10, sun yi garkuwa da manoma

Mayakan ta'addancin Boko Haram sun kashe farar hula goma a wani hari da suka kai wani kauyen da ke yankin arewa maso gabas, majiyoyin tsaro daga yankin suka tabbatar a ranar Litinin.

Babakura Kolo, shugaban wata kungiyar yaki da ta'addancin da ke samun goyon bayan gwamnati, ya sanar da AFP cewa mayakan sun kai harin a ranar Lahadin da ta gabata.

Kolo ya ce sun shiga kauyen Kurmari, mai nisan kilomita 40 tsakaninsa da Maiduguri a yammacin Lahadi inda suka kashe mutum hudu yayin da suke bacci.

Maharan basu yi amfani da bindigogi ba ta yadda dakarun sojin da ke kusa ba za su ji ba, wani mutum mai suna Ibrahim Liman yace.

Wannan yankin ya kasance wurin da mayakan suka dade suna kai harin kunar bakin wake ko kuma hari da bindigogi.

A wani bangaren kuwa, 'yan ta'addan sun kone mutum uku da ransu inda suka kashe daya a wani kauye da ke wajen Maiduguri a ranar Lahadi, SaharaReporters ta wallafa.

An yi garkuwa da manoma biyu wadanda mayakan ta'addancin suka tarar suna noma a gonakinsu.

A cikin kwanakin nan dai, mayakan sun matsantawa manoma lamba inda suke bin su har gonakinsu suna kashewa ko garkuwa da su.

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 10, sun yi garkuwa da manoma
Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kashe mutum 10, sun yi garkuwa da manoma. Hoto daga SaharaReporters
Source: Twitter

KU KARANTA: Dalilin da yasa gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur - Fadar shugaban kasa

A wani labari na daban, a kalla mutum hudu cikin 'yan gudun hijira mayakan Boko haram suka yi awon gaba da su a yayin da suke gonakinsu a kusa da Maiduguri a ranar Talata, wasu majiyoyi suka tabbatar.

An gano cewa, mayakan Boko Haram sun kutsa Dalwa da ke kusa da yankin Molai a Maiduguri da ke jihar Borno. Sun kai wa manoman hari tare da yin awon gaba da hudu daga ciki.

Ganau ba jiyau ba da suka bada labari, sun ce mayakan ta'addancin sun kai harin a kan babura ga manoman da basu da mataimaka.

Mallam Babagana, wanda ya sha da kyar daga harin 'yan ta'addan ya ce a kan idonsa aka kwashe mutane hudun. Da kanshi ya bayyana wa iyalan wadanda lamarin ya shafa.

KU KARANTA: Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue

Hakan kuwa ya janyo tashin hankali a sansanin 'yan gudun hijira na Bakassi.

"A yau, daya ga watan Satumban 2020, wurin karfe 4:20 na yammaci mayakan Boko Haram suka kutsa gonakin 'yan gudun hijira da ke Dalwa a Molai suka yi awon gaba da mutane hudu," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel