Rashin lafiya: An fitar da ministan ilimi, Adamu Adamu, kasar waje

Rashin lafiya: An fitar da ministan ilimi, Adamu Adamu, kasar waje

- An fitar da ministan ilimi, Adamu Adamu, zuwa kasar Jamus domin a duba lafiyarsa, kamar yadda SaharaReporters ta rawaito

- SaharaReporters ta rawaito cewa wannan shine karo na uku da aka fitar da ministan zuwa turai a 'yan watannin baya bayan nan

- Adamu Adamu ya na daga cikin minsitoci da ke da kusanci da kuma kyakyawar alaka da shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Sahara Reporters ta wallafa rahoton cewa yanzu haka ministan ilimi na kasa, Adamu Adamu, ya na zaman jinya a kasar Jamus.

A cikin wani rahoto da SaharaReporters ta wallafa ranar Litinin, ta bayyana cewa an kwantar da Adamu Adamu a wani asibiti da ke birnin Berlin.

A cewar SaharaReporters, wannan shine karo na uku da aka fitar da ministan zuwa kasar Jamus domin a duba lafiyarsa tun bayan barkewar annobar korona.

Wata majiya ta sanar da SaharaReporters cewa ministan yana fama da matsalar koda.

Sai dai, duk da hakan, har yanzu babu tabbacin wanne ciwone ya ke yawan fitar da ministan zuwa Turai domin a duba lafiyarsa.

Harkoki da yawa da suka shafi bangaren ilimi sun tsaya cak saboda ministan baya nan.

Jaridar SaharaReporters ta wallafa cewa shirye-shiryen komawa makaranta sun tsaya a yayin da ake tsammanin dawowar ministan nan bada dadewa ba.

Rashin lafiya: An fitar da ministan ilimi, Adamu Adamu, kasar waje
Ministan ilimi, Adamu Adamu
Asali: UGC

"Wannan shine karo na uku da aka fitar da ministan zuwa kasar Jamus tun bayan barkewar annobar korona.

"A daya daga cikin irin tafiye-tafiyen da ya yi, ya yi amfani da wani karamin jirgi mallakar wani tsohon shugaban wata jami'ar Najeriya.

DUBA WANNAN: Za ka fuskanci bakar zanga-zanga - Kungiyar daliban Najeriya ta aikawa Buhari sako mai zafi

DUBA WANNAN: Buhari zai kaddamar da shirin tallafawa 'yan kasuwa da N50,000 a kowanne wata

"Yanzu hakan ya na kwance zaman jinya a wani asibiti da ke birnin Berlin a kasar Jamus, amma ana boye maganar, musamman dalilin yawan fitarsa zuwa Turai a kwanakin baya bayan nan.

"Abubuwa da dama da suka shafi bangaren ilimi, musamman shirin bude makarantu, sun tsaya saboda ministan ilimi ba ya nan," a cewar majiyar gwamnati, kamar yadda SaharaReporters ta wallafa.

Adama Adamu ya na daga cikin ministoci ma su kusanci da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

An yi tsammanin cewa Buhari zai nada Adamu Adamu a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa bayan mutuwar marigayi Abba Kyari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel