Rundunar soji ta kashe yan ta’adda 9, sun ceto mutum 7 a Gwoza

Rundunar soji ta kashe yan ta’adda 9, sun ceto mutum 7 a Gwoza

- Dakarun Operation Lafiya Dole da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas sun kashe yan ta’adda tara a yayin wata kakkaba a karamar hukumar Gwoza da ke Borno

- Rundunar Bataliya 192 da taimakon rundunar sama ne suka kai hari kan yan ta'addan a garin Hamdaga Makaranta da ke Gwoza

- Dakarun sun kakkabe gine-gine tara da gonakin Boko Haram da ISWAP a yankin

Rundunar sojin Najeriya a ranar Litinin ta ce dakarunta na Operation Lafiya Dole da ke yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabas sun kashe yan ta’adda tara a yayin wata kakkaba a karamar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

Jagoran labarai na ayyukan rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Ya ce bisa bayanai abun dogaro da suka samu kan ayyukan yan ta’addan a garin Hamdaga Makaranta da ke Gwoza, rundunar Bataliya 192 da taimakon rundunar sama a ranar 6 ga watan Satumba 2020, sun kai mamaya wajen.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

Rundunar soji ta kashe yan ta’adda 9, sun ceto mutum 7 a Gwoza
Rundunar soji ta kashe yan ta’adda 9, sun ceto mutum 7 a Gwoza
Source: UGC

Ya ce dakarun sojin sun yi nasara kan yan ta’addan inda suka kashe mutum biyar yayinda sauran suka tsere da raunukan bindiga.

Rundunar sun kakkabe gine-gine tara da gonakin Boko Haram da ISWAP a yankin.

Ya um ace rundunar sun cceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su wadanda suka hada da mata biyu da yara biyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gidaje, shaguna sun kone kurmus yayinda motar tanka ta kama da wuta a jihar Neja

A wani labari makamancin wannan, rundunar sojoji na Operation Whirl Stroke a jihohin Benue da Nasarawa sun kashe yan bindiga biyar yayinda suka kama wasu takwas.

Manjo Janar John Enenche, ya ce an kashe yan bindiga hudu a yayin wani mamaya da aka kai mabuyarsu a Tse Agi, karamar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benue.

Ya kuma bayyana cewa an kashe daya daga cikin yan bindigan a lokacin da dakarun suka kai farmaki sansaninsu da ke iyakar Benue-Nasarawa.

Eneche wanda ya bayyana cewa an samo alburusai da dama a yayin arangaman, ya yaba ma jama’a a kan bayar da muhimman bayanai na kwararru wanda ya sa aka cimma nasara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel