Akwai yiwuwar shan-inna da gudawa su kama yara saboda dakatar da rigakafi

Akwai yiwuwar shan-inna da gudawa su kama yara saboda dakatar da rigakafi

Gwamnati ta takaita zirga-zirga a kokarin rage yaduwar cutar nan ta COVID-19 a kasar nan.

Miliyoyin kananan yara a Najeriya su na fuskantar barazanar kamuwa da cututtuka irinsu shan-inna, kyanda, gudawa da wasu ciwon a halin da ake ciki.

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa takaita zirga-zirga da aka yi a domin dakile yaduwar annobar COVID-19, ya dakatar da allurorin rigakafi da aka saba yi wa yara.

Jaridar ta ce an fasa ko akalla an dakatar da wasu rigakafin da aka tsara za a yi a shekarar nan saboda annobar COVID-19 da ta harbi mutane fiye da 50, 000.

Wannan ya sa ake ganin cewa cutar COVID-19 ta zo da matsalar da za ta iya jawo ci-ma-baya a cigaban da aka samu a yakin da Najeriya ta yi da cutar shan-inna.

KU KARANTA: COVID-19 ta na shiga Kauyuka a Kaduna - Gwamna

A shekarar nan ne hukumar lafiya ta Duniya ta tabbatar babu ragowar masu cutar shan-inna a Najeriya.

Masana da masu ruwa da tsaki a harkar lafiya sun yi gargadi cewa ana samun matsanancin karancin yaran da ake yi wa rigakafi saboda annobar da ake fama da ita a yanzu.

WHO da UNICEF sun ce “Iyayen yara su na kwiwyar su bar gida saboda takunkumin da aka sa na zirga-zirga, da karancin bayanai, ga tsoron kamuwa da kwayar cutar COVID-19.”

Shugaban Africa Budget Health Network, Dr. Aminu Magashi ya ce annobar COVID-19 ya jawo matsala wajen rigakafi a dalilin karancin PPE da alawus din ma'aikata.

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnati ta yi maganar bude makarantu

Ba tare da rigakafi ba, yara da-dama za su zama cikin hadarin kamuwa da kyanda da wasu cututtuka inji wani kwararren likita.

“Alal misali, yara da yawa za su samu cutar sanyi ta 'pneumonia', wanda ta ke kisa cikin sauri. Wasu za su yi fama da gudawa da amai, da rashin samun kayan gina jiki.”

Dr. Magashi ya ce: “Wasu za su iya kamuwa da cututtukan idanu, da kunne da ciwon kwakwalwa, wasunsu za su iya samun ciwon da ake kira encephalitis.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: