Shugaban kasa 2023: Sanata Abaribe ya gargadi Kudu akan kalaman Elrufai

Shugaban kasa 2023: Sanata Abaribe ya gargadi Kudu akan kalaman Elrufai

- Sanata Abaribe ya ce kada yankin kudu ta yarda da goyon bayan da El-Rufai ya bayar na cewa a mika mata shugabancin kasar

- Gwamnan na Kaduna ya ce yankin kudu ya kamata a mika wa shugabancin kasa a 2023

- Abaribe, shugaban marasa rinjaye a majalisa ya kuma bayyana Peter Obi da Charles Soludo a matsayin shugabannin siyasa na Igbo da ka iya zama Shugaban kasa

Sanata Enyinnaya Harcourt Abaribe, shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, ya shawarci yankin kudu a kan yarda da furucin gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan shugabancin 2023, a cewar jaridar Vanguard.

Legit.ng ta rahoto a baya cewa Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa yankin kudu ce za ta samar da shugaban kasa na gaba.

Gwamnan Kadunan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, a wata hira da sashin Hausa na BBC.

KU KARANTA KUMA: Sojoji sun kashe yan bindiga 5, sun kuma kama 8 a Nasarawa da Benue

Sai dai Vanguard ta ruwaito cewa Abaribe ya ce: “suna so su yi amfani da kan Igbo su fasa kwakwa.”

Shugaban kasa 2023: Sanata Abaribe ya gargadi Kudu akan kalaman Elrufai
Shugaban kasa 2023: Sanata Abaribe ya gargadi Kudu akan kalaman Elrufai Hoto: El-Rufai/Vanguard
Source: UGC

Don haka, jigon na PDP ya ambaci sunayen wasu shugabannin siyasa na Igbo irin su Peter Obi da Charles Solido a matsayin wadanda ka iya zama shugaban kasa.

Ya kuma bayyana cewa: “Dan Igbo ne kadai zai iya hada Najeriya cikin aminci.”

A wani rahoton kuma, ministan kwadago, Dr Chris Nwabueze Ngige, ya bayyana cewa za a cimma nasarar samar da shugaban kasa dan kabilar Igbo a 2023.

KU KARANTA KUMA: An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta (Hotuna)

Ministan ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Sun ta wallafa a ranar Alhamis, 20 ga watan Agusta.

Sai dai Ngige ya ce ba zai so ya yi magana sosai a kai ba tunda shugaban kasa Muhammadu Buhari bai riga ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu ba.

Har ila yau, wata kungiyar matasan Igbo ta lamuncewa wasu yan takara biyu daga kudu domin su zama shugaban kasa a 2023.

Kungiyar bayan taron hadin gwiwa da ta gudanar a Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi a ranar Asabar, 15 ga watan Agusta, ta bayar da shawarar tsayar da ministan kimiya da fasaha, Dr Ogbonnaya Onu da gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi a matsayin yan tsakarar Igbo da za su gaji Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel