Kada ku koma ajujuwa idan aka bude makarantu, NUT ga malamai

Kada ku koma ajujuwa idan aka bude makarantu, NUT ga malamai

- Kungiyar malaman Najeriya (NUT) reshen babbar birnin tarayya ta umurci malaman makarantun firamare a birnin da kada su koma bakin aiki idan aka sake bude makarantu

- Shugaban kungiyar na FCT, Kwamrad Stephen Knabayi ne ya bayar da wannan umurnin a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba

- Ya ce sun yanke wannan hukunci ne saboda shugabannin kananan hukumomin yankin sun ki biyan malaman firamaren karancin albashi

Shugaban kungiyar malaman Najeriya (NUT) reshen babbar birnin tarayya, Kwamrad Stephen Knabayi, ya umurci malaman makarantun firamare a birnin da kada su koma bakin aiki a duk sanda aka sake bude makarantu domin ci gaba da karatu.

Kwamrad Knabayi ya yi wannan kira ne yayinda yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wani taron gaggawa na shugabannin kungiyar a gidan malamai da ke Gwagwalada a ranar Asabar.

Ya ce hukuncin kungiyar na umurtan malaman su zauna a gida ya biyo bayan gazawar shugabannin hukumomin yankin na wajen biyan mafi karancin albashi na malamai.

Ministan birnin tarayya, Muhammad Musa Bello, ya biya sabon karancin albashi don haka ya kamata shugabannin hukumomin su yi koyi da shi.

Kada ku koma ajujuwa idan aka bude makarantu, NUT ga malamai
Kada ku koma ajujuwa idan aka bude makarantu, NUT ga malamai
Asali: Original

Ya bayyana cewa kungiyar ta gana da karamar ministar birnin tarayya, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu da shugabannin hukumomi shida da sauran masu ruwa da tsaki.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

Amma ya ce basu cimma matsaya ba na biyan karancin albashi ga malaman makarantun firamare, don haka suka yanke shawarar tafiya yajin aiki idan aka bude makarantu.

“Mun ga cewa shugabannin hukumomin basu dauki lamarin da muhimmanci ba kuma basu damu da jin dadin malamai ba. Tunda gwamnatin birnin tarayya bata da lokaci wajen biyan karancin albashi, muna sanya ran shugabannin hukumomin za su yi koyi suma su aikata hakan,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewar duk da kiran kungiyar kan shugabannin hukumomin shida na su biya malaman firamare karancin albashi, wanda yace suna ta fama sama da watanni 17, sun ki aikata hakan.

Ya ce malaman sakandare za su taya malaman makarantun firamare wajen tafiya yajin aiki.

KU KARANTA KUMA: Babbar nasara: Yan sanda sun damke gagararrun ƴan fashi, sun kwace makamai da kuɗi

A wani labarin, Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta fara biyan N30,000 a matsayin ma fi karancin albashi ga 'yan fansho a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng