Kano: Mutanen da aka zartar da kisa a kansu daga farkon shekara zuwa yanzu

Kano: Mutanen da aka zartar da kisa a kansu daga farkon shekara zuwa yanzu

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa mutane tara Alkalai su ka yankewa hukuncin kisa a wannan shekara ta 2020.

Mai magana da yawun bakin ma’aikatar shari’a, Baba Jibo-Ibrahim, ya shaidawa jaridar Premium Times wannan a karshen makon jiya.

Mista Baba Jibo-Ibrahim ya ce babu ko guda daga cikin wadannan mutane da aka samu da laifi da aka kai ga zartar da hukuncin a kansa.

An samu wadannan mutum tara da laifi ne tsakanin watan Junairu zuwa Agustan da ta gabata kamar yadda jami’in ya bayyana.

Baba Jibo-Ibrahim ya ce abin da ya hana a zartar da hukuncin kisan da ke kansu shi ne dukkaninsu sun daukaka kara zuwa kotun gaba.

BBC Hausa ta ce bakwai daga cikin wadannan mutane da Alkalai su ka yankewa hukuncin kisa, an same su ne da laifin kashe rai.

KU KARANTA: An gano Ma’aikacin ya shafe shekaru ya na cin albashi biyu

Kano: Mutanen da aka zartar da kisa a kansu daga farkon shekara zuwa yanzu
Kotun shari'a su na aiki a Jihar Kano
Asali: Facebook

Ragowar biyun sun aikata laifin fyade ne da kuma yi wa addini batanaci a jihar Kano.

Ga sunayensu nan da laifuffukan da su ka yi kamar yadda mu ka samu rahoto.

1. Ali Abdullahi – Laifin kisa-kai

2. Yakubu Dalha – Laifin kisan-kai

3. Abdullahi Isyaku – Laifin kisan-kai

4. Mujahid Sa’id – Laifin kisan-kai

5. Naziru Ya’u – Laifin kisan-kai

6. Shehu Ado Shehu – Laifin kisan-kai

7. Isah Auta – Laifin kisan-kai

Duka wadannan an same su ne da laifin kashe rai, don haka aka zartar masu da hukuncin kisa.

8. Yahaya Aminu-Shariff – Laifin batanci ga addini

9. Mati Abdu – Laifin fyade

Yahaya Aminu-Shariff shi ne wanda aka samu da laifi kwanan nan bayan ya yi wa addini batanci, an yankewa Shariff da Mati hukunci ne a babban kotun shari’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel