Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue

Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue

A kokarin ganin dawwamar zaman lafiya da yaki da ta'addanci, 'yan bindiga, satar shanu da sauran miyagun lamurran da ke aukuwa a yankin arewa na tsakiya, rundunar Operation Whirl Stroke ta cafke 'yan bindiga hudu tare da samo miyagun makamai a samamen da ta kai wa sansaninsu.

Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa
Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa. Hoto daga DHQ
Source: Twitter

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na tsaro, Manjo janar John Enenche ya fitar a wata takarda, ya ce wannan nasarar ta samu a samamen da rundunar ta kai a ranar 6 ga watan Satumban 2020.

Ya tabbatar da cewa bayanan sirri na inda sansanin yake ne ya kai wa zakakuran dakarun. Sun yi nasarar kashe daya daga ciki inda sauran suka fada daji da raunika.

"A daya daga cikin samamen da rundunar opertaion Whirl Stroke da ke Guma a jihar Benue da kuma wadanda ke Keana a jihar Nasarawa suka kai a ranar 6 ga watan Satumba.

"Sun kai samame inda suka gano sansanin 'yan bindigar ne a dajin Guma da ke tsakanin iyakar jihar Benue da Nasarawa bayan bayanan sirrin da suka samu.

"Cike da kwarewa da gogewa, zakakuran sojin sun gano sansanin inda suka bude wa 'yan bindigar wutar.

"A cikin haka ne suka kashe daya daga cikin 'yan bindigar amma wasu suka tsere da miyagun raunika cikin dajin.

"Dakarun sun samo bindiga kirar AK 47 guda daya, carbin harsasai, bindigar toka daya da wayoyin salula uku. Babu kakkautawa suka ragargaza sansanin," takardar tace.

Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa
Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa. Hoto daga DHQ
Source: Twitter

KU KARANTA: Ruwan kudi a shagalin bikin Hanan Buhari ya janyo cece-kuce (Bidiyo)

Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa
Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa. Hoto daga DHQ
Source: Twitter

Hakazalika, dakarun da aka tura Gagbe da ke karamar hukumar Gwer ta arewa a jihar Benue, sun kai wani samame dayan sansanin 'yan bindigar da ke yankin Tse Agi.

Sun yi nasarar shiga sansanin inda suka cafke 'yan bindiga hudu da miyagun makamai.

"Zakakuran sojin sun isa wani sansani da ke karamar hukumar Gwer ta yamma inda suka damke wasu 'yan bindiga hudu.

"Sun samu bindiga kirar AK 47 daya, carbin harsasanta biyu da wasu harsasai 46 a maboyar. Sun ragargaza sansanin tare da kama 'yan bindigar wadanda za su mika ga hukumomin da suka dace domin ladabtarwa," takardar ta kara da cewa.

Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa
Sojoji sun cafke 'yan bindiga 4 da miyagun makamai, sun ragargaza sansaninsu a Benue da Nasarawa. Hoto daga DHQ
Source: Twitter

Hukumar tsaro ta kasa na jinjinawa zakakurai kuma jajirtattun sojin Najeriya a kan kokarinsu na tabbatar da wanzuwar tsaro a yankin arewa.

Ta yi kira ga jama'a da su samar da bayanan da suka dace ga jami'an tsaron domin ci gaban tabbatuwar nasara da wanzar da tsaro a fadin kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel