'Yan bindiga sun kutsa fadar babban basarake, sun harba a kalla mutum 60

'Yan bindiga sun kutsa fadar babban basarake, sun harba a kalla mutum 60

Wadansu bata-gari da ake zargin 'yan bindiga ne a ranar Lahadi sun kutsa fadar Isiu da ke Ikorodu a jihar Legas, inda suka yi yunkurin garkuwa da sabon basarake bayan da suka dinga harbe-harbe.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ya ruwaito cewa Sarki Okukayode Raji ya karba wannan sarautar daga ofishin kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Legas, Wale Ahmed, a ranar 24 ga watan Augustan 2020.

Basaraken ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa, 'yan daban sun isa da yawansu dauke da makamai kafin isowar kungiyar 'yan sintiri wadanda suka tarwatsa mummunan nufinsu.

"Haka kawai mun fara ganin wasu fuskoki da wasu matasa suna zuwa kusa da fadar dauke da makamai.

"A yayin da suka kusanto mu, sun fara harbe-harbe. Daya daga cikin 'ya'yana maza ya samu mummunan rauni.

"Gidana, motata da wasu mutane da suka zo kawo gaisuwa duk an raunata su.

"A kalla an harba mutum 60, wadanda suka samu raunika duk an mika su asibiti," basaraken yace.

'Yan bindiga sun kutsa fadar babban basarake, sun harba a kalla mutum 60
'Yan bindiga sun kutsa fadar babban basarake, sun harba a kalla mutum 60. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mutum mafi muni a fadin duniya ya aura mata ta 3 (Hotuna)

Sarkin ya ce ya tuntubi shugaban 'yan sandan yankin domin neman taimako, jaridar Solacebase ta wallafa.

"Sun amsa ni, daga baya amma sun turo jami'ansu suna sintiri a yankin. An kama wasu mutum uku da ake zargi da hannu a ciki," yace.

Basaraken ya yi kira ga shugabannin yankin da su hada kai da jama'arsu domin shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Ya kara kira ga gwamnatin jihar Legas da ta saka hannu wurin inganta tsaro domin gujewa sake faruwar hakan.

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne a ranar Lahadi, sun kai hari yankin Adara da ke Buda a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna. Sun kashe Rabaren Alubara Audu da wasu mutum biyu tare da sace wasu mutum biyar.

Awemi Dio Maisamari, shugaban kungiyar kabilar Adara, a wata takarda ya jajanta aukuwar lamarin a yankin sannan ya yi kira ga hukumomi da su kawo karshen lamarin.

Kamar yadda Maisamari yace, "mugun harin da aka kai ya lashe rayukan mutum uku. Sun yi garkuwa da wasu mutum biyar a yankin.

"Wurin daidai wannan lokacin, 'yan ta'addan sun yi garkuwa da mutum biyar daga yankin Kemara Rimi a gundumar Buda."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel