Wani sojan Najeriya ya wallafa hotunan abokan aikinsa da Boko Haram suka kashe a Maiduguri

Wani sojan Najeriya ya wallafa hotunan abokan aikinsa da Boko Haram suka kashe a Maiduguri

Wani sojan Najeriya mai suna Emmanuel, a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, ya nuna alhini a kan mutuwar wasu abokan aikinsa da suka mutu a filin daga.

Emmanuel ya wallafa hotunan abokan nasa wadanda ya ce sun mutu a yayin arangama da ‘yan ta’addan Boko Haram a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Ku tuna cewa akalla sojoji ashirin aka kashe sannan wasu da dama suka bata bayan hare-hare mabanbanta da kungiyar ISWAP wacce ta balle daga Boko Haram suka kai Borno a makon da ya gabata.

A cewar Emmanuel, sojojin sun “mutu a filin daga yayin arangama da mayakan Boko Haram a Maiduguri.”

Ga hotunan sojojin a kasa:

Wani sojan Najeriya ya wallafa hotunan abokan aikinsa da Boko Haram suka kashe a Maiduguri
Wani sojan Najeriya ya wallafa hotunan abokan aikinsa da Boko Haram suka kashe a Maiduguri
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: 'Duk lauya Musulmi da ya ce zai kare wanda ya zagi Annabi Muhammadu (SAW) ya kafurta' - Malami

A baya mun kawo maku cewa an yi artabu a tsakanin sojojin Najeriya da mayakan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Kungiyar ta ISWAP ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe sojojin Najeriya akalla guda 20 a hare-hare biyu da suka kai kan sojojin a jihar Borno, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kai hari wani sansanin soji da ke Magumeri cikin motoci da aka girke manyan bindigogi a kansu.

Garin Magumeri na a tsawon kimanin kilomita hamsin daga Maiduguri, babban birnin Jihar ta Borno.

A cikin wata sanarwa, kungiyar ISWAP ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe sojoji goma da kuma kwace makamai da motocin soji a yayin arangama da suka yi.

Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta kashe wasu karin sojoji 10 a wani kwanton-bauna kan ayarin sojojin a kusa da kauyen Kuros-Kauwa da ke yankin Baga.

An tattaro cewa dukkanin lamuran biyu sun faru ne a ranar Talata da ta gabata.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa majiyoyinsa sun tabbatar masa da cewa sojoji tara mayakan suka kashe a Magumeri.

Hakazalika rundunar sojin ta yi ikirarin kashe mayakan kungiyar a wani hari ta sama da dakarunta suka kai da jiragen yaki kan sansanin yan ta'addan a kauyen Kaza, kusa da Gulumba-Gana a yankin Bama cikin jihar ta Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel