Mun kashe N31 biliyan cikin watanni 4 don yaki da korona – Gwamnatin tarayya

Mun kashe N31 biliyan cikin watanni 4 don yaki da korona – Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayar da bayani kan yadda ta kashe N36.3bn na kudin korona

- Babban ma’ajin gwamnnati, Ahmed Idris, ya ce gaba daya an kasha kaso 84 na kudin, akalla N30.5bn, yayinda N5.9bn ya yi saura a asusun

- Sai dai rahoton gwamnatin bai gamsar da kungiyoyin kare hakkin dan adam da suka nemi jin bayanin yadda aka kashe kudaden ba

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta “kashe kudi N30,540,563,571.09, wanda ya yi daidai 84% na naira biliyan 36.3 na kudaden jama’a da gudunmawar da ta karba domin magance lamarin kororna tsakanin 1 ga watan Afrilun 2020 da 31 ga watan Yulin 2020, kudin da ya yi saura a yanzu naira biliyan 5.9 ne.”

Babban ma’ajin gwamnatin tarayya, Agmed Idris, ya bayyana hakan a yayinda yake amsa bukatar da kungiyoyin Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) da Connected Development (CODE) suka nema mai kwanan wata 10 ga Agustan 2020.

Da suke martani ga Mista Idris a ranar 4 ga watan Satumban 2020, dauke da hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare da shugaban CODE, Hamzat Lawal, kungiyoyin sun ce:

“Mun kula cewa kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19 ya kasha naira biliyan 22, sannan jihohi 36 sun kashe naira biliyan 7 domin tallafawa shirye-shiryensu na COVID-19.”

Mun kashe N31 biliyan cikin watanni 4 don yaki da korona – Gwamnatin tarayya
Mun kashe N31 biliyan cikin watanni 4 don yaki da korona – Gwamnatin tarayya Hoto: Sunnewsonline.com
Source: UGC

Kungiyoyin sun ce: “Mun kuma kula cewa rundunar sojin saman Najeriya ta kasha naira miliyan 877 wajen jigilar kayayyaki domin tallafawa ayyukan COVID-19; yayinda rundunar yan sanda ta kashe naira miliyan 500 kan kayayyakin kare kai. An biya N17,865.09 kan chajin banki.”

Martanin kungiyar ya zo kamar haka: “Sai dai kuma, mun lura cewa takardun da aiko mana baya dauke da cikakken bayani kamar yadda bukatar take a takardarmu na ranar 10 ga watan Agusta 2020, ciki harda cikakken bayani da rabe-raben adadin yan Najeriya wadanda suka amfana kai tsaye daga wannan kashe kudin, da kuma bayani kan tsare-tsaren kashe sauran naira biliyan 5.9 da ke asusun yaki da korona.

“Zai kyautu a lura cewa talakan Najeriya 115 sun bayar da gudunmawa tsakanin N1 da N100 domin tallafawa hukumomi a kokarinsu na yaki da korona, duk da cewar kasar ce mafi talauci da ta ci gaba da jurewa radadin annobar korona.

KU KARANTA KUMA: Za mu binne Oshiomhole ta fuskacin siyasa, in ji Obaseki

“Wannan gagarumin darasi ne ga jami’an gwamnati da yan siyasa game da lamarin aikin gwamnati a kasar mutum. Ya kuma aika da gagarumin sako game da bukatar yan siyasa su dunga kallon kujerar gwamnati a matsayin wani dama na yi wa kasa hidima, ba wai wajen yin yadda aka dama, sata da kuma karkatar da kudaden mutane zuwa ga aljihunsu don amfanin kansu ba.

“Muna maraba da jajircewar da kuka nuna na yin komai a bayyana da kuma bayar da bayani kan kudaden, sannan muna fatan sauran jami’ai da hukumomin gwamnati za su yi koyi da wannan misali mai kyau ta hanyar mutunta dokar FoI.

“Za mu yi farin cikin samun karin bayani kai tsaye da kuma Karin bayani kan N34.4bn da aka kashe tsakanin watan Afrilu da Yuli, da kuma bayani kan abunda za a yi da ragowar biliyan 5.9 na asusun tallafin korona.

“Cikin N36.3bn na kudaden jama’a da wanda aka bayar na gudunmawa, N1.4bn ya fito daga yan Naeriya da kamfanoni ta asusun bankunan zamani, yayinda aka samu N536m ta babban bakin Najeriya (CBN). Tallafin sun hada da N89m da N279m daga majalisar dattawa da majalisar wakilai.

“Bugu da kari, kasar China wacce cibiyaar kasuwanci a Najeriya ta bayar da N48m; hukumar daidaita man fetur ta bayar da N50m yayinda hukumar kula da ci gaban Najeriya ta bayar N70m.

“Za mu yi farin ciki idan aka yi mana karin bayani cikin kwanaki bakwai na wallafa wannan wasika. Idan ba mu ji daga gare ba toh, SERAP da COD za su dauki matakin day a kamata a karkashin dokar FoI don tursasa ku ba bukatar hadin kai.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel