Ambaliyar ruwa: Mutum 20 sun mutu, gidaje da gonaki 50,000 sun salwanta a Jigawa

Ambaliyar ruwa: Mutum 20 sun mutu, gidaje da gonaki 50,000 sun salwanta a Jigawa

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa, SEMA, ta sanar da cewa yawan mutanen da suka mutu ya kai 2 tare da dubban gidaje da gonakin da suka lalace sakamakon gagarumar ambaliyar da ta auku a jihar.

Sakataren hukumar, Mr Yusuf Sani Babura, ya sanar wa manema labarai a Dutse cewa ambaliyar, wanda ke aukuwa duk shekara, ya shafi 17 daga cikin kananan hukumomi 27 na jihar wanda hakan ya jefa rayukan jama'a mazauna garuruwan cikin rudani.

Ya kara da cewa mafi yawar wanda suka rasa rayukan su yara ne kanana sakamakon rugujewar gine gine.

Ambaliyar ruwa: Mutum 20 sun mutu, gidaje da gonaki 50,000 sun salwanta a Jigawa
Ambaliyar ruwa: Mutum 20 sun mutu, gidaje da gonaki 50,000 sun salwanta a Jigawa. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Ya ce haka; "Ambaliyar da ta saba aukuwa duk shekara ta halakar da gidaje 5,000 gonaki da yawa kuma sun nutse inda amfanin gona daya hada da su masara, gero, dawa da shinkafa suka lalace a kananan hukumomi da yawa da ke jihar sakamakon gagarumar ambaliyar ruwan data auku a satin daya gabata".

A cewar sakataren, gwamantin jihar ta bawa hukumar SEMA umurnin ta gaggauta samar da taimako ga garuruwan da abun ya shafa. "an tanadar da wurin na wucin gadi ga wadanda abun ya shafa wanda ya hada da makarantu, masallatai da kuma gidajen 'yan uwa".

Ya kuma bayyana cewa tuni an samar da agaji da taimako na gaggawa ga wadanda abun ya shafa wanda ya hada da abinci, magunguna, gadaje, kwalekwale da kuma wajen zama na wucin gadi, ya kara da cewa kuma gwamnatin jihar tana yin iyakar kokarin ta wajen ganin cewa an kawar da al'amarin zuwa wani sashe na jihar.

A bangarensa gwamnan jihar ta Jigawa Badaru Abubakar ya nuna matukar damuwan sa game da aukuwar wannan gagarumar ambaliyan da ta shafa sassan jihar wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama da kuma asarar dubban gidaje da gonaki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel