Mai Dalilin Aure: Yadda nake hada maza da mata masu son aure a Kano

Mai Dalilin Aure: Yadda nake hada maza da mata masu son aure a Kano

Malam Rabiu Ado Indabawa dattijo ne a garin Kano wanda ya kware a hada maza da mata masu neman wanda za su aura. Babu shakka ana samun dacewa idan da rabo ta hanyarsa.

"Bayan rabuwar aurena har sau biyu, na cire rai da zan samu mata tagari, don haka ne na daina yi wa mata tayin soyayyata.

"Hakan ya ci gaba har sai da na hadu da Malam Rabi'u Ado Indabawa, wanda ya hada ni da mata ta a yanzu a shekaru uku da suka gabata," Malam Yarima Muhammad ya sanar da jaridar Daily Trust.

A halin yanzu Muhammad yana da 'ya'ya biyu daga aurensa na shekaru uku. Ya bayyana yadda ya cire rai daga samun mata tagari bayan aurensa ya mutu a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Bayan cin karo da yayi da sanarwar mai dalili, ya mika bukatarsa na neman mace tagari inda aka hada shi da matarsa ta yanzu.

Muhammad yana daya daga cikin daruruwan mutanen da suka hadu da matansu ko mazansu na aure ta hannun Malam Rabiu Ado Indabawa.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, a kalla mutum 50 zuwa 70 na kiran Malam Rabiu a cikin birnin Kano a kowacce rana domin neman mace ko mijin aure.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A halin yanzu 'Mai dalilin aure' yana ta kara shahara a babban birnin Dabo inda wasu iyayen ke kai 'ya'yansu da kansu domin a nema musu miji.

Mai dalilin aure: Yadda nake hada maza da mata masu son aure a Kano
Mai dalilin aure: Yadda nake hada maza da mata masu son aure a Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mutum mafi muni a fadin duniya ya aura mata ta 3 (Hotuna)

Malam Indabawa wanda yake cikin shekarunsa na hamsin da doriya, ya ce ya mayar da hankali wurin hada aure a Kano sakamakon yawan zawarawan da suke garin.

Kara karanta wannan

Yadda Naga Matata Tana Saduwa da Ɗan Uwana, Miji Ya Faɗa Wa Kotu Komai, Ya Nemi Raba Auren

A kalla a kan yi aure wanda Mai Dalili ya hada, guda biyar a kowanne sati a cikin babban birnin na Dabo.

"Na fada wannan harkar ne domin ganin cewa duk wanda ke son yin aure bai rasa wanda zai aura ba. Ban fara domin in samu kudi ba, na fara ne domin nemawa jama'a mafita.

"Bana son ganin mutum na son yin aure da gaske amma bashi da wanda zai aura yana ta nema," Indabawa yace.

Malam Indabawa ya ce, "Na saka kamar tallar abinda nake yi a wurare daban-daban na birnin, na kan saka lambar wayata kuma duk mai bukata zai iya kira.

"Idan mai son miji ko mata ya kira ni, na kan saka lokacin ganin shi da kaina. Bayan tattaunawa na kan gane cewa mutumin kirki ne ko akasin hakan.

"Idan na gamsu da yanayin mutum, na kan tambaya irin wanda yake so. Ko daga nan ina gane manufar da mutumya zo da ita. Daga nan na kan bai wa wanda na ga ya dace da shi lambar waya.

Kara karanta wannan

Ganduje Ba Zai Ruguza Mani Gida ba, ko da a kan Layin Lantarki aka Gina Inji Rarara

"Daga tattaunawarsu, su kan fahimci ko za su iya zama da juna. Idan an dace, daga nan sai iyaye su sani a fara shirin aure."

“Ina tsayawa daga nan, kuma bana rakiyar neman aure. Iyaye kan kawo 'ya'yansu zawarawa ko 'yan mata wadanda suka isa aure domin samun miji.

“Jama'a da yawa sun yi aure ta hakan. Ba zan iya cewa ga yawan wandanda suka yi auren ba amma a cikin shekaru biyar da suka gabata, a kalla ana samun mutum uku da ke aure a kowanne mako," ya yi bayani.

Da aka tambayesa ko yana karbar kudi idan zai yi wannan hadin, ya ce ba ya karbar ko sisi. Amma bayan auren idan ma'auratan sun ga ya dace, su kan bashi kyauta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Mai Shekaru 19 Ya Yi Garkuwa Da Kansa Ya Karɓi Fansar Naira Miliyan 1 Daga Mahaifinsa A Adamawa

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: