Aikin Hajji: NAHCON za ta rage yawan kwanakin da Musulman Najeriya ke shafewa a Saudiyya

Aikin Hajji: NAHCON za ta rage yawan kwanakin da Musulman Najeriya ke shafewa a Saudiyya

Hukumar jin dadn alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da kammala shirinta na rage adadin kwanakin da 'yan Najeriya ke shafewa a kasar Saudiyya yayin aikin Hajji.

Shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, ne ya sanar da hakan yayin wata ziyarar ganin wasu aiyuka da ake yi a sansanin hukumar da ke sassan kasar nan.

A cikin wani jawabi da kakakin NAHCON, Fatima Usara, ta fitar, ta bayyana cewa Zikrullah ya samu rakiyar wasu manyan kwamishinoni guda uku da wasu ma'aikatan hukumar NAHCOM.

Jawabin ya kara da cewa tawagar ta wakilan NAHCON, a karkashin jagorancin Zikrullah, ta ziyarci jihohin Bauchi, Kwara, Kano, Jigawa, da Katsina.

Jawabin ya kara da cewa, tawagar NAHCON ta ziyarci ofishin gwamnoni da fadar sarakunan gargajiya a dukkan jihohin da suka ziyarta domin neman hadin kansu wajen cimma manufofin hukumar NAHCON.

Da ya ke gabatar da jawabi, Zikrullah ya bukaci samun hadin kan gwamnatoci da mahukunta a gabanin kaddamar da sabon tsarin asusun gata ga maniyyata aikin Hajji na gaba da kuma kafa cibiyar horon alhazai.

Aikin Hajji: NAHCON za ta rage yawan kwanakin da Musulman Najeriya ke shafewa a Saudiyya
Maniyyata aikin Hajji
Asali: UGC

Kazalika, ya kara da cewa NAHCON za ta sabunta tare da zamanantar da mu'amalarta da maniyyata ta hanyoyin amfani da sabbin dabarun fasahar zamani.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Abinda wani Magidanci ya fada bayan an kamashi yana lalata 'yar shekara 4 a Masallaci

A cewar Zikrullah, NAHCON za ta cigaba da neman hanyoyin da zasu mayar da kudin aikin Hajji ya zama daidai da aljihun jama'a.

Zikrullah ya kara da cewa burin hukumar NAHCON shine ganin duk wani Musulmin Najeriya mai burin zuwa aikin Hajji ya samu sukunin iya biyan kudin kujera.

Shugaban na NAHCON ya yi kira ga maniyyata da su daina karya kasuwancinsu ko kuma shiga cikin rigimar kudi domin su hada kudin biyan kujerar zuwa aikin Hajji.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel