Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa

Wani mutum ɗan ƙasar Zimbabwe ya sha duka bayan an kama shi dumu-dumu yana ƙoƙarin zina da matar mai gidansa.

A yayin da fusatattun mazan da suka kama shi suke 'ɗumamama masa jiki', matar da aka kama su tare ta sulale ta bar shi yana ɗanɗana kuɗarsa shi kaɗai.

Mutumin da ke sanye da riga mai launin 'orange' ne ya tona asirin matar da yaron mai gidanta.

Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa
Bidiyo: An kama wani dumu-dumu yana ƙoƙarin yin zina da matar mai gidansa. Hoto daga LIB
Source: Twitter

A yayin da ake masa duka, an jiyo muryar wasu daga cikin mazajen suna yi masa faɗa a kan mene zai sa ya ci amanan abokinsa kuma mai gidansa.

Bayan afkuwar wannan ruguntsumin, an gano cewa mijin matar duk da haka yana son ta dawo gidansa su cigaba da zaman aure kamar yadda shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Ga bidiyon a ƙasa:

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta amince da buɗe makarantu a Najeriya

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji wani mutumi da ya kashe wasu mata guda biyu ya boye gawarwakin su a cikin firji yana fuskantar hukuncin kisa.

Mutumin mai suna Zahid Younis an yanke masa hukuncin kisa, ta hanyar yin shekaru 38 a gidan yari.

Gawarwakin Henriett Szucs da kuma na Mihrican Mustafa an samo su a gidan Zahid a garin Canning, yankin gabashin London, a watan Afrilun shekarar 2019.

An ruwaito cewa yayi rikici da matan kafin ranar da ya kashe su duka su biyu.

Gawar daya daga cikinsu Henriett Szucs na ajiye a cikin firji tsawon shekara uku kafin 'yan sanda su gano ta gidan saurayin dan shekara 36 a gabashin London.

Ms Szucs, mai shekaru 34 da take 'yar asalin kasar Hungary, ganin da aka yi mata na karshe shine a watan Agustan shekarar 2016, kuma an tabbatar cewa ta tafi ta zauna da Younis ne a gidansa.

Mace ta biyun kuma wacce take tana da 'ya'ya guda uku mai suna Mihrican Mustafa, mai shekaru 38, ita ma ba a kara jin duriyarta ba tun a cikin watan Mayun shekarar 2018.

Ms Szucs da Ms Mustafa, duka mata ne da suke yin wata irin rayuwa, inda suke barin gidajensu, shan miyagun kwayoyi da sauransu, kamar dai yadda kotun ta samu rahoto.

An ruwaito cewa Younis ya sayi wannan firji ne jim kadan bayan ya kashe Ms Szucs saboda kawai ya ajiye gawarta a ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel