Tarihi ya maimaita kansa: An yi wa Shugaba Buhari raddi kan tashin kayan abinci
A cikin makon nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zargi dillalai da jawo tashin farashin kayan abinci da ake fuskanta a Najeriya.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da ya bada sanarwar umarnin fitar da ton 30, 000 na masara domin tallafawa masu harkar abincin dabbobi.
Jaridar The Cable ta ce ya kamata ace mutane sun yabawa Muhammadu Buhari da yunkurin da ya ke yi, amma a karshe sai aka ji jama’a su na caccakarsa.
Ga ainihin abin da Buhari ya fada: “Duk wadannan matsaloli da ake fuskanta, mafi takaicinsu shi ne halin wasu dillalai marasa gaskiya da kuma masu saida abinci da su ke shiga tsakanin manoma da jama’a da su ke kirkiro wahalar kaya saboda su saida abinci da tsada sosai.”
Mutane sun lalubo wata tsohuwar jaridar Sunday Herald ta shekarar 1984, su ka tunawa shugaban kasar yadda ya saba zargin dillalai da ‘yan kasuwa da laifi.
Yayin da ake tsakiyar fama da yunwa a watan Junairun 1984, Muhammadu Buhari a lokacin ya na shugaban kasa na mulkin soja, ya bada irin makamancin wannan uzuri.
KU KARANTA: “Shugabannin rikon kwaryan APC za su jawo danyen rikici a Zamfara"
Jama’a da-dama sun zargi shugaban kasar da gujewa nauyinsa, mun tsakuro maku kadan daga cikin abubuwan da mutane su ke fada a kafofin sada zumunta na zamani.
David Adebiyi ya ce za a iya shawo kan matsalolin dilallai idan gwamnati ta tsaida farashin kaya a kasuwa, sannan aka samu hukuma da za ta rika sa idanu.
Wani Bawan Allah a shafin Twitter ya ce, “Babu abin da ya hada dillalai da tashin farashi, su na cin moriyar rashin gaskiyar da ake tafkawa ne a gwamnatinka.” Ya ce: “A dai yi nazari da kyau.”
Tempest Onwe cewa ya yi da karin kudin wuta da man fetur, babu amfanin fito da masara a rabawa manoma.
Malam IS Alhassan ya rubuta: “Ba laifin ‘yan kasuwa ba ne kurum. Wannan gwamnati ta na ta fama da hauhawar farashin kaya tun da ta hau mulki. Litar man fetur a N162, ya wannan ba zai jawo tashin farashi ba?”
Shi kuma wani cewa ya yi, “Manufofin gwamnatinka sun fi duk wata annoba illa. Kayan abinci sun tashi, kudin wuta ya tashi, farashin mai ya tashi. Kuma ka na zargin wasu da laifi?”
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng