Bauchi: Sojoji 2 sun rasu, 1 yana kwance rai a hannun Allah bayan hatsarin mota

Bauchi: Sojoji 2 sun rasu, 1 yana kwance rai a hannun Allah bayan hatsarin mota

Jami'ai biyu na rundunar sojin saman Najeriya sun rasa ransu sakamakon mummunan hatsarin motar da aka tafka a ranar Litinin a jihar Bauchi.

Daya daga cikin jami'an ya samu miyagun raunika yayin hatsarin.

Jaridar The punch ta gano cewa, lamarin ya ritsa da jami'an rundunar sojin saman Najeriya har su uku.

Suna tafiya a wata mota kirar Volkswagen Golf inda wata mota kirar Ford Galaxy dauke da fasinjoji shida ta auka musu.

Daya daga cikin jami'an ya rasu a take, na biyun ya rasu bayan an mika su asibitin sojin sama kuma ya fara samun taimakon masana kiwon lafiya.

Na ukun kuwa a halin yanzu yana asibiti inda yake samun taimako.

An gano cewa, motar sojojin ta tsage gida biyu a yayin da mummunan hatsarin ya auku.

Kwamandan hukumar kiyaye hadurran kan titi na tarayya na yankin, Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce hatsarin ya faru a kauyen Gubi Gari da ke kan babbar hanyar Bauchi zuwa Kano.

Duk wani kokari na tuntubar hukumar sojin saman Najeriya, ya gagara.

Kakakin runduna ta musamman da ke Bauchi, FC Ezenyi, bai yi martani a kan sakonnin kar ta kwana da kuma wadanda aka dinga tura masa ta manhajar WhatsApp ba.

Bauchi: Sojoji 2 sun rasu, 1 yana kwance rai a hannun Allah bayan hatsarin mota
Bauchi: Sojoji 2 sun rasu, 1 yana kwance rai a hannun Allah bayan hatsarin mota. Hoto daga Defence HQ
Source: UGC

KU KARANTA: Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da ya yanke wa budurwa nonuwa a otal (Hotuna)

A wani labari na daban, a kokarin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya tare da yaki da ta'addanci a kasar nan, zakakuran dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Accord ta lallasa 'yan bindiga a jihar Kaduna.

sun kai samame a yankin Jeka Da Rabi da ke babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja,inda suka halaka 'yan bindigar dajin hudu.

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo janar John Enenche, ya bayyana a wata takarda da ya fitar a ranar uku ga watan Satumban 2020, yace, " dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Accord, sun kai wa 'yan bindiga samame.

"Sun yi nasarar halaka hudu daga ciki a yankin Jeka Da Rabi da ke kan babban titin Abuja zuwa Kaduna."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel