Boko Haram: Sojoji da mayakan ISWAP sun yi karon batta a Borno, da yawa sun mutu

Boko Haram: Sojoji da mayakan ISWAP sun yi karon batta a Borno, da yawa sun mutu

- Labari da muke samu ya nuna cewa an yi arangama tsakanin sojojin Najeriya da mayakan kungiyar ISWAP a jihar Borno

- Kungiyar yan ta’adda ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe sojojin Najeriya akalla guda 20 a hare-hare biyu da suka kai kan sojojin

- Sai dai zuwa yanzu ba a ji ta bakin rundunar sojin ba

Rahotanni sun kawo cewa an yi artabu a tsakanin sojojin Najeriya da mayakan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Kungiyar ta ISWAP ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe sojojin Najeriya akalla guda 20 a hare-hare biyu da suka kai kan sojojin a jihar Borno, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kai hari wani sansanin soji da ke Magumeri cikin motoci da aka girke manyan bindigogi a kansu.

Garin Magumeri na a tsawon kimanin kilomita hamsin daga Maiduguri, babban birnin Jihar ta Borno.

A cikin wata sanarwa, kungiyar ISWAP ta yi ikirarin cewa mayakanta sun kashe sojoji goma da kuma kwace makamai da motocin soji a yayin arangama da suka yi.

Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta kashe wasu karin sojoji 10 a wani kwanton-bauna kan ayarin sojojin a kusa da kauyen Kuros-Kauwa da ke yankin Baga.

Boko Haram: Sojoji da mayakan ISWAP sun yi karon batta a Borno, da yawa sun mutu
Boko Haram: Sojoji da mayakan ISWAP sun yi karon batta a Borno, da yawa sun mutu
Asali: UGC

An tattaro cewa dukkanin lamuran biyu sun faru ne a ranar Talata.

Zuwa yanzu babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin masu tayar da kayar bayan.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa majiyoyinsa sun tabbatar masa da cewa sojoji tara mayakan suka kashe a Magumeri.

Zuwa yanzu rundunar sojin bata ce komai ba kan lamarin.

Sai dai rundunar sojin ta yi ikirarin kashe mayakan kungiyar a wani hari ta sama da dakarunta suka kai da jiragen yaki kan sansanin yan ta'addan a kauyen Kaza, kusa da Gulumba-Gana a yankin Bama cikin jihar ta Borno.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: FG ta saussata dokar hana zirga zirga, ta mayar 12am zuwa 4am

Shi ma farmakin, a ranar Talata sojojin suka kai, wato ranar da kungiyar ta ISWAP ta yi ikirarin kashe sojojin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel