Harin Kagara: Rundunar 'yan sanda ta hallaka 'yan bindiga 6

Harin Kagara: Rundunar 'yan sanda ta hallaka 'yan bindiga 6

Kwamishinan 'yan sandan jihar Neja, Adamu Hassan, ya yi karin bayani dangane da harin da 'yan bindiga suka kai wani banki da ke garin Kagara na jihar Neja a ranar Laraba.

Da ya kai ziyarar gani da ido zuwa Kagara ranar Alhamis, Hassan ya sanar da cewa rundunar 'yan sanda ta kashe shidda daga cikin 'yan bindigar da suka kai hari garin ranar Laraba.

Kazalika, kwamishinan ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe dan sanda guda daya, wani jami'in tsaro na kamfani, dan bijilanti da kuma wani mutum.

Ya kara da cewar wani yaro guda daya ya mutu sakamakon razanar da ya yi a lokacin da 'yan bindigar suka kai harin.

Kwamishina Hassan ya ce 'yan bindigar sun tsere sun bar baburansu guda hudu bayan sun ga jami'an 'yan sanda na kokarin cimmasu a yayin da suke musayar wuta.

"Na jinjinawa ma'aikatanmu da ke aiki a ofishin 'yan sanda na Kagara saboda karfin gwuiwar da suka nuna wajen tunkarar 'yan bindigar ba tare da tsoron cewa suna dauke da muggan makamai ba.

"Hedikwatar 'yan sanda ta jiha zata cigaba da bayar da dukkan gudunmawar da ta dace ga jami'anta a kowanne bangare na jihar Neja domin yaki da 'yan ta'adda da batagari," a cewar Kwamishinan.

Harin Kagara: Rundunar 'yan sanda ta hallaka 'yan bindiga 6
Harin Kagara: Rundunar 'yan sanda ta hallaka 'yan bindiga 6
Source: Twitter

A daren ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa 'yan bindiga sun kai farmaki a garin Kagara, shelkwatar karamar hukumar Rafi, jihar Niger.

Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa 'yan bindigar sun tarwatsa tawagar wasu matasa da ke wasan kwallo kafin daga bisani su kai farmaki wani banki da ke cikin garin Kagara.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Abinda Magidanci ya fada bayan an kamashi yana lalata 'yar shekara 4 a Masallaci

Ita kuwa jaridar The Nation, ta ruwaito cewa akalla 'yan bindiga fiye da 70 ne haye a kan babura suka mamaye garin Kagara, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi kuma sun shafe kusan sa'o'i shidda suna cin karensu babu babbaka.

A yayin da wata majiya da ta yiwa wakilin jaridar kiran gaggawa, don shaida masa abunda ke faruwa, wakilin ya ce yana iya jiyo karar harbe harben bindiga da inda ya ke a garin Kagara.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa da yawa daga cikin mazauna garin sun gudu sun bar gidajensu, tare da buya a cikin gonaki, don tsira da rayukansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel