Yanzu yanzu: FG ta saussata dokar hana zirga zirga, ta mayar 12am zuwa 4am

Yanzu yanzu: FG ta saussata dokar hana zirga zirga, ta mayar 12am zuwa 4am

Gwamnatin tarayya ta gyara dokar hana zirga-zirga daga 12:00 na tsakar dare zuwa 4:00 na asubahi, yayinda take ci gaba da sassauta matakan kulle da ta sa don hana yaduwar COVID-19 a kasar.

Shugaban kwamitin shugaban kasa kan COVID-19, Dr Sani Aliyu, ya bayyana hakan a ranar Alhamis lokacin wani taro a Abuja.

A watan Yuni, PTF ya rage yawan kullen kasa baki daya daga 10:00 na safe zuwa 4:00 na asubahi a kokarin takaita taron jama’a da kuma takaita yaduwar cutar.

Dr Aliyu, ya yi bayanin cewa dokar bai shafi masu aiki na musamman da masu dawowa daga kasashen waje ba.

Yanzu yanzu: FG ta saussata dokar hana zirga zirga, ta mayar 12am zuwa 4am
Yanzu yanzu: FG ta saussata dokar hana zirga zirga, ta mayar 12am zuwa 4am
Asali: Facebook

“Muna gyara dokar takaita zirga-zirgan ne domin ya fara daga karfe 12:00 na tsakar dare zuwa 4:00 na asuba a fadin kasar, zai fara aiki daga 12:00 na daren yau.

“Wannan bai shafi mutanen da ke ayyuka na musamman ba da matafiya na kasa da kasa da ka iya dawowa daga kasashen waje.”

Ya kuma bayyana cewa an dage duk wani takaitawa da aka sanya ga matafiya na mota kuma kasuwanni a fadin kasar na iya ayyukansu a kullun.

Har ila yau, shugaban PTF din ya bayyana cewa wuraren kallo na sinima da wuraren wasanni na iya aiki, inda ya cire wuraren shan giya da gidajen rawa.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin

A gefe guda mun ji cewa gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bawa Hukumar Kula da Masu Yi wa Ƙasa Hidima, NYSC, ta fara shirye-shiryen buɗe sansanin horaswarta a dukkan faɗin ƙasar.

Shugaban kwamitin ƴaki da korona ta shugaban ƙasa, Dakta Sani Aliyu ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Alhamis yayin jawabin kwamitin a Abuja.

Aliyu ya ce hukumar ta NYSC ta fara shirin buɗe sansanonin ta tare da inganta matakan kare yaɗuwar cutar da zarar makarantu sun buɗe.

Ya ce, "A bangaren hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima, NYSC ta ɗora a kan matakan kariya da ake da su a yanzu ta fara shirin buɗe sansanonin ta da zarar an buɗe makarantu.

"Muna kan tsare dokokin ta yadda ba za a samu ɓullar annobar korona ba da zarar an buɗe sansanonin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel