Katsina: 'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 50, sun samo shanu 220

Katsina: 'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 50, sun samo shanu 220

Rundunar 'yan sandan jiihar Katsina a yammacin Alhamis sun cafke 'yan bindiga fiye da 50 tare da kwato shanun sata 220 a kashi na biyun kokarinsu na yakar 'yan bindiga, fashi da makami, satar shanu, garkuwa da mutane da wasu nau''in laifuka a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Sanusi Buba Sanusi, ya sanar da manema labarai a wata tattaunawa da suka yi a hedkwatarsu a Katsina cewa, rundunar ta samo bindigogi kirar AK 47 guda 9, bindigar toka 20, ababen hawa biyu da babura 20.

Ya ce, "A tsawon lokacin nan, rundunar 'yan sandan sun yi ayyukansu a wurare daban-daban kuma sun yi nasarar kamo 'yan bindigar da suka addabi jihar Katsina."

"Hakazalika, an samu kudi har N685,000 kuma rundunar ta kashe 'yan bindiga 15 tare da ceto mutum 20 da aka yi garkuwa da su."

A bangaren yaki da fyade a jihar, ya sanar da cewa rundunar ta cafke mutum 140 a jihar da take zargi da fyade kuma ta mika 87 gaban kotu.

Katsina: 'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 50, sun samo shanu 220
Katsina: 'Yan sanda sun damke 'yan bindiga 50, sun samo shanu 220. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Kano: Yadda aka halaka wani mutum a teburin mai shayi

A wani labari na daban, jama'a mazauna kauyen Sabon Garin Nasarawa da ke karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina sun zama jajirtattu, jaridar Katsina Post ta wallafa.

Jama'ar sun tattara duk wata jarumtarsu tare da yin gaba-gaba da wasu 'yan bindigar daji wadanda suka kai musu hari a sa'o'in farko na ranar Talata da ta gabata.

Kamar yadda rahotanni daga Katsina Post suka bayyana, 'yan bindigar masu tarin yawa a kan babura sun tsinkayi kauyen wurin karfe 12:30 na ranar Talata.

Sun yi awon gaba da dabbobinsu, kayan abinci da abubuwa masu muhimmanci na jama'ar kauyen. Amma kuma bayan da 'yan bindigar suka sakankance cewa sun yi nasara, matasan sun yi jarumta inda suka zagaye gonaki tare da dazuzzukan da ke kusa.

Rahotanni sun bayyana cewa, matasan sun yi nasarar kashe daya daga cikin 'yan bindigar tare da kwato dabbobinsu da suka sace.

Amma kuma, a wannan karon, 'yan bindigar sun kashe daya daga cikin mazauna kauyen tare da raunata wani, wanda a halin yanzu yake gadon asbiti inda ake kula da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel