Buhari: Miyagun ‘Yan kasuwa su ka jawo tashin farashin abinci don cin riba

Buhari: Miyagun ‘Yan kasuwa su ka jawo tashin farashin abinci don cin riba

Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya koka game da halin da al’umma su ka samu kansu a sakamakon tashin farashin kayan abinci.

Shugaban kasar ya yi magana a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, 2020, ta bakin Malam Garba Shehu, babban mai taimaka masa wajen harkokin yada labarai.

Hadimin ya ke cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san halin da mutanensa su ke ciki, kuma ya na kokarin daukar matakin rage radadin da aka shiga.

Duk da kokarin gwamnatin tarayya na ganin an samu isasshen abinci, Buhari ya ce wannan shekara ta 2020 ta zo da abubuwan da su ka girgiza Duniyar Bil Adama.

A cewar shugaban kasar, wasu ‘yan kasuwa daga ketare su na da laifi wajen tsadar kayan abinci da ake gani, baya ga annobar COVID-19 da ta taba tattalin Duniya.

Wata matsalar da aka fuskanta ita ce rashin samun kayan yin takin zamani a kan kari, hakan ya sa amfanin gona su ka rube tun kafin a kai ko ina inji shugaban kasar.

KU KARANTA: Ya kamata a nuna rashin goyon baya ga karin kudin wuta - Sani

Buhari: Miyagun ‘Yan kasuwa su ka jawo tashin farashin abinci don cin riba
Shugaban Najeriya ya ce 'yan kasuwa su ka jawo tsadar kaya
Asali: Facebook

Bayan haka, kamfanoni su na sayen kayan gona tun kafin su karasa, wannan ya kara jawo tsadar abinci.

“Duk wadannan matsaloli da ake fuskanta, mafi takaicinsu shi ne halin wasu dillalai marasa gaskiya (wadanda an gano wasunsu da-dama ‘yan kasar waje ne) da kuma masu saida abinci da su ke shiga tsakanin manoma da jama’a da su ke kirkiro wahalar kaya saboda su saida abinci da tsada sosai.” inji Shehu.

“Wajen shawo kan wadannan matsaloli, gwamnati a kokarin saukaka kasuwanci, ta guji haramta adana kaya, saboda tsoron jawo jama’a su guji adana kaya a dakunan ajiya na zamani.”

Shugaban Najeriyar ya hada-kai da manyan kungiyoyin manoma da masu harkar hatsi, za a shigo da abinci daga ketare da nufin ganin an ga karshen wannan tsadar kaya.

Dazu kun ji cewa ana kuka da karin farashin wutar lantarki da sabon karin kudin man fetur da aka yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng