Femi Falana SAN ya sa an karbo takardu, zai daukaka kara a shari’ar Aminu Shariff
- Ana kokarin daukaka karar Yahaya Aminu Shariff zuwa gaban babban kotu
- Kotu ta samu Yahaya Aminu Shariff da laifin cin mutuncin musulunci a baya
- Wannan ya sa Alkalin karamin kotun shari’a ya yanke masa hukuncin kisa
Ana kishin-kishin din cewa shahararren lauyan nan, Femi Fakana SAN, zai tsayawa Yahaya Aminu Shariff wanda aka yankewa hukucin kisan-kai.
Babban Lauyan zai kare wannan matashi mai shekaru 22 da haihuwa da Alkali ya samu da laifin cin mutuncin addinin musulunci a jihar Kano kwanakin baya.
Rahotannin da su ke zuwa mana a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, 2020, sun bayyana cewa Femi Falana ya samu karbar takardun wannan shari’a da ake yi.
Hakan na zuwa ne makonni uku da samun Aminu Shariff da laifi a gaban wani kotun shari’a. Falana zai tsaya wajen ganin an daukaka kara domin a saki matashin.
Mai magana da yawun bakin bangaren shari’a na jihar Kano, Babajido Ibrahim, ya sanar da manema labarai wannan cigaba da aka samu a shari'ar dazu da rana.
KU KARANTA: Kungiyar Musulmai ta bankado ‘makarkashiyar’ Kiristanta
Mista Babajido Ibrahim ya ce takardun wannan kara da zaman kotun da aka yi sun kai ga Femi Falana, a madadin wani Lauya da ya aiko ya wakilce sa a jihar Kano.
An gabatarwa wakilin Femi Falana SAN wadannan takardu ne a ranar 2 ga watan Satumba. Wannan zai bada damar lauyan ya kare wanda ake tuhuma a gaban kuliya.
Falana wanda ya yi fice wajen kare hakkin Bil Adama, zai duba hukuncin da Alkalin kotu ya yanke a watan Agusta, daga nan ya garzaya kotu, ya daukaka wannan shari’a.
Wannan shari’a ta jawo ce-ce-ku-ce har a ketare, inda wasu su ke ganin bai kamata a yankewa mutum hukuncin kisa a kasar da kowa ya ke da ‘yancin yin magana ba.
A gefe guda, masana addinin musulunci sun yaba da hukuncin da Khadi Aliyu Muhammad na kotun shari’a da ke Hausawa ya yi, sun ce haka addinin musulunci ya tanada.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng