Hotuna: Mawaki Akon ya bayyana kudurinshi na gina birnin N2.3 tiriliyan wanda ya sakawa suna Akon City

Hotuna: Mawaki Akon ya bayyana kudurinshi na gina birnin N2.3 tiriliyan wanda ya sakawa suna Akon City

- Mawakin nan dan kasar Senegal dake zaune a kasar Amurka, Akon, ya bayyana shirin shi na gina birni mai sunan shi

- Birnin wanda aka bayyana cewa zai ci kudi har kimanin naira tiriliyan 2.3, za a gina shi a kasar Senegal

- Akon wanda yayi hira da manema labarai ya ce abinda ya sanya zai gina wannan birni, shine saboda ya sanya mutanen dake kasashen ketare dawowa Afrika

Fitaccen mawakin nan dan kasar Senegal dake zaune a kasar Amurka, Akon, yayi magana akan shirin shi na gina birni wanda za a sanyawa suna Akon City a kasar Senegal.

Da yake magana da manema labarai a wajen wani taro da aka gabatar ranar Litinin, 31 ga watan Agust, 2020, ya ce babban abinda ya sanya zai gina birnin shine domin mutanen Afrika dake kasashen Turai su dawo gida.

Akon ya ce a lokacin da ya tashi a Amurka, inda iyayenshi suka koma a lokacin yana dan shekara bakwai, ya sha ganin 'yan Afrika da dama dake zaune a can wadanda basu san al'adarsu ba, hakan ya sanya ya kuduri aniyar gina birnin da zai sanya mutane su dawo gida.

Hotuna: Mawaki Akon ya bayyana kudurinshi na gina birnin N2.3 tiriliyan wanda ya sakawa suna Akon City
Hotuna: Mawaki Akon ya bayyana kudurinshi na gina birnin N2.3 tiriliyan wanda ya sakawa suna Akon City
Asali: Instagram

Ya ce: "Wato ina so na gina birni irin wannan wanda zai basu kwarin guiwa su gane cewa akwai gida a gida."

Birnin wanda aka yi masa tsari na zamani, wani mai zane ne mai suna Hussein Bakri ya zana, ance akwai asibitoci, otel-otel, makarantun jami'a, wajen kallo da shakatawa da dai sauransu.

Akon kuma ya ce birnin zai zama da kauye wanda ke dauke da al'adu na 'yan Afrika. Mawakin wanda asalin sunansa shine, Aliaume Damala Badaka Akon Thiam, ya ce: "Idan kazo daga Amurka ko Turai kuma kaji kana so ka ziyarci Afrika muna so Senegal ta zama wajen da zaka fara tsayawa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel