Haduwar Ganduje da Osinbajo a Abuja: An bayyana batutuwan da suka tattauna akai

Haduwar Ganduje da Osinbajo a Abuja: An bayyana batutuwan da suka tattauna akai

- Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a fadar shugaban kasa

- Sun tattauna ne a kan matsalolin da ke kewaye da tsaro da harkar ilimi a jihar

- Gwamna Ganduje ya tabbatar da lamarin inda ya ce ya gabatarwa da mataimakin shugaban kasar wani rahoto

Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya tattauna da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan lamuran da ke kewaye da tsaro da harkar ilimi a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Ganduje, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a fadar Shugaban kasa, ya ce ya zo korowa mataimakin Shugaban kasa jawabi kan kokarin da ake yin a magance matsalolin.

Ya bayyana cewa rundunar soji na iya bakin kokarinta kuma ana tallafa mata wajen korar yan ta’adda daga dajin Falgore.

Gwamnan ya ce: “Kawai don na koro mai bayani ne game da lamuran da ke a jihar Kano, musamman game da garkuwa da mutane, ta’addanci, fashi da makami da sauran ayyukan assha a yankin.

“Na kuma gabatar masa da wani rahoto; muna kula, akwai hukumomin tsaro sosai a Kano, suna aiki tukuru.

Haduwar Ganduje da Osinbajo a Abuja: An bayyana batutuwan da suka tattauna akai
Haduwar Ganduje da Osinbajo a Abuja: An bayyana batutuwan da suka tattauna akai
Asali: UGC

“Matsala daya da muke da shi shine na dajin Falgore wanda muke samar da gini na horar da sojoji domin hana ‘yan bindiga kwace wannan wuri.

“Muna kokari sosai a kan haka, saboda haka a takaice wannan shine abunda na zo tattaunawa da shi.”

Ya bayyana cewa mataimakin Shugaban kasar ya yi farin ciki kuma ya samu karfin gwiwa da rahoton.

Kan tattalin arzikin garin Kano, ya bayyana cewa babbar birni ce, don haka, dole ne a karfafa ayyukan kasuwanci.

KU KARANTA KUMA: Sirika ya yi babban gyara a ma'aikatar sufuri, ya kori daraktoci

A cewarsa, dukkanin kasuwanni a Kano a cike suke, don haka akwai bukatar a bunkasa su zuwa sauran wurare.

Ganduje ya kuma yi magana game da naira miliyan 880 da aka raba ma hukumomi 44 na jihar Kano don gyaran makarantun firamare.

Ya bayyana cewa babban dalilin shirin shine domin karfafawa jama’a gwiwar shiga shirin ci gaba a harkar ilimin jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel