Kalaman batanci: Matawalle ya yi barazanar tura 'yan adawa gidan yari a Zamfara

Kalaman batanci: Matawalle ya yi barazanar tura 'yan adawa gidan yari a Zamfara

- Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya gargadi ƴan jam'iyyun adawa su 'iya bakinsu' ko kuma su tafi gidan yarin

- Matawalle ya yi wannan gargadin ne a ranar Laraba a Gusau yayin da ya ke maraba da wasu ƴan APC da suka dawo PDP

- Ya ce wasu ƴan siyasa da ba a yayin su yanzu sun koma furta kalaman batanci da cin mutuncin mutane kuma ba zai amince da hakan ba

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya gargadi yan jam'iyyar adawa ta All Progressives Congress, APC, da sauran jam'iyyu su kula da abinda suka furtawa ko kuma su tafi gidan yari.

Matawalle ya yi wannan fadi hakan ne yayin da ya ke yi wa wasu dubban ƴan APC da suka dawo PDP jawabi ranar Laraba a Gusau.

Ku kula da abinda ku ke faɗa ko ku tafi gidan yar - Matawalle ga ƴan adawa
Ku kula da abinda ku ke faɗa ko ku tafi gidan yar - Matawalle ga ƴan adawa
Asali: Facebook

Gwamnan ya ce zai kama duk wani ɗan siyasa da ya ɓata masa suna ya kuma mika shi ga hukuma don bincike.

Matawalle ya ce, "Idan ka san ba za ka iya kare abinda ka faɗa ba, gara ka dena ɓata wa mutane suna domin zan bada umurnin a kama duk mai yin hakan kuma zai tafi gidan yari."

Ya ce wasu ƴan siyasa sun koma furta kalaman ɓatanci da cin mutunci saboda siyasa kawai don sun rasa mulki.

DUBA WANNAN: Kutse a gonar Obasanjo: An gurfanar da dattijo mai shekaru 60

Ya gargadi irin wannan ƴan siyasar suyi nesa daga jihar ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Matawalle ya kuma gargadi irin wannan ƴan siyasar su dena yi wa harkar tsaro zagon ƙasa a jihar inda ya ce, "ba zan amince da hakan ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel