Aikin me Gwamnatin Buhari ta yi a Yankin Arewa tun da ta hau mulki? – ‘Yan Twitter

Aikin me Gwamnatin Buhari ta yi a Yankin Arewa tun da ta hau mulki? – ‘Yan Twitter

Wasu Bayin Allah sun fito cikin makon nan su na jimami tare da kalubalantar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta nuna ayyukan da ta yi a Arewa.

‘Yan Arewacin Najeriya su ne su ka fi bada kaso mai tsoka a tafiyar jam’iyyar APC, sai dai kuma wasu Matasan yankin su na ganin babu abin da yankin ya amfana.

Wadannan matasa sun fito kan dandalin sada zumunta su na kalubalantar gwamnatin APC ta bayyana irin moriyar da su ka ci tun da aka kafa gwamnati a 2015.

Wasu su na zargin cewa akwai yaudara a lamarin gwamnatin APC, ganin yadda ake fama da rashin tsaro da kuma tsadar kayan abinci, game da darajar Naira da ta karye.

Haka zalika wasu kuma sun rika bankado irin gudumuwa da goyon bayan da su ka bada wajen hawan shugaba Buhari mulki a 2015, su na yi masa gorin cewa an bada su.

Wani Bawan Allah mai suna Musbey a Twitter ya ce: “Goodluck Jonathan ya yi wa Arewacin Najeriya fiye da abin da Buhari da su ka zaba ya yi masu. #Northernprojects

Auta Musa ya ke cewa: “Zan iya tuna lokacin da na sadaukar da motata wajen yi wa Buhari kamfe, ina zaton zai ba mu mamaki da ayyuka a Arewa, ba mu san akasin haka za mu gani ba.” #NorthernProjects

KU KARANTA: COVID-19: Dattijon Arewa ya bukaci Buhari da Gwamnoni 36 su bi doka

A ra’ayin Mahmud Waziri, gwamnatin tarayya ta zage ne da ayyuka a kudancin Najeriya, su kuma mutanen Arewa, an bar su da mukaman da ba su amfanar jama’a.

Jabir Ishaq kuwa tambaya ya ke yi: “Ina aikin wutan Taraba, ina labarin wutan Mambila, ina tashar Baro, ina aka kwana a titin Maiduguri zuwa Kano da Abuja zuwa Kaduna?”

Malam Zannah ya ce a lokacin da Buhari ya ke neman mulki, ya yi ta yi wa Arewa alkawura, amma da ya zama shugaba babu aikin da aka gani, ya ce Buhari ka gaza.

M. Farees ya ce gwamnatin Buhari ta gaza a komai; tsaro, tattalin arziki da ilmi, komai ya rushe.

Irinsu Sani Waspapin sun ce ba su da-na-sanin kin zaben Goodluck Ebele Jonathan a 2015, amma @MBuhari ya dauki hanyar bada kunya, #NorthernProjects

Shi kuwa Dr. Kabir Aliyu ya kare shugaban kasar, ya jero irin alherin gwamnatinsa a yankin da ya fito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel