Damfara: EFCC ta sake gurfanar da Mama Boko Haram tare da wasu mutum 4

Damfara: EFCC ta sake gurfanar da Mama Boko Haram tare da wasu mutum 4

Ofishin hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) na jihar Borno, ya gurfanar da Aisha Alkali Wakil, wacce aka fi sani da Mama Boko Haram a gaban wata babbar kotu da ke jihar Borno.

An gurfanar da Mama Boko Haram a gaban Mai shari'a Aisha Kumaliya sakamakon zarginta da ake yi da laifuka hudu da suka hada da: hada kai wurin zamba, bada bayanan bogi da kuma damfarar kudi har N6 miliyan.

A wani zaman kotun, lauyan masu gurfanarwa, Mukhtar Ali ahmad, ya bukaci kotun da ta soke zargin farko wanda aka mika mata a ranar 3 da 10 ga watan Maris na 2020, ta maye gurbinsa da na ranar 18 ga watan Maris 2020.

Mai shari'a Kumaliya ta maye gurbin tsoffin zargin da sabbin, sannan ta umarci a karantowa wadanda ake zargin laifukansu, jaridar Vanguard ta wallafa.

Damfara: EFCC ta sake gurfanar da Mama Boko Haram tare da wasu mutum 4
Damfara: EFCC ta sake gurfanar da Mama Boko Haram tare da wasu mutum 4. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Makasan maza: Yadda matasa suka bi 'yan bindiga, suka kashe 1 tare da kwato shanunsu

Daya daga cikin abubuwa da ake zarginsu da shi sun hada da, "Cewa Aisha Wakil, Tahiru Alhaji Saidu Daura da Lawal Shoyode, yayin da suke shugabantar wata kungiyar tallafi mai zaman kanta mai suna Complete Care anda Aid Foundation, tsakanin watan Oktoba da Nuwamban 2018 a Maiduguri, sun damfari wani mutum mai suna Alhaji Bukar Kachalla.

"Sun bukacesa da ya kawo musu mota kirar Toyota Camry 2012 mai darajar kudi har naira miliyan shida. Wannan laifin ya ci karo da sashi na 320 kuma abun hukuntawa ne a sashin 332 na dokokin Penal Code na jihar Borno."

Sun musanta aikata wannan laifin dukkansu. Hakan yasa lauyan mutum na biyu da na uku da ke kare kansa, H. Waziri, ya bukaci kotun da ta dage shari'ar domin ya samu duba sabbin zargin.

Mai shari'a Kumalliya ta dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Satumban 2020.

An fara gurfanar da Mama Boko Haram tare da Lawal Shoyode a ranar 4 ga watan Disamban 2019. An bayyana musu abubuwan da ake zarginsu da shi amma sun musanta aikata laifukan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel