Sirika ya yi babban gyara a ma'aikatar sufuri, ya kori daraktoci

Sirika ya yi babban gyara a ma'aikatar sufuri, ya kori daraktoci

- Rahotanni sun kawo cewa an sallami wasu daraktoci a ma'aikatar jirgin sama na Najeriya

- Hukuncin ya kasance ne saboda gagarumin sauye-sauye da gwamnatin tarayya ta yi a hukumar

- Gwamnatin tarayya ta yi sauye-sauye makamancin haka a ma'aikatar a watan Fabrairun 2017 kuma har ya shafi daraktoci a wancan lokacin

Wani rahoto daga jaridar Vanguard ya nuna cewa gwamnatin tarayya ta yi gagarumin sauye-sauye a ma'aikatar jirgin sama na Najeriya (NCAA), a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba.

A cewar rahoton, an hade wasu daraktocin ma'aikatar, yayinda aka raba wasu da ayyukansu.

Rahoton ya kuma bayyana cewa babu wata sanarwa daga mahukunta kan lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Sirika ya yi babban gyara a ma'aikatar sufuri, ya kori daraktoci
Sirika ya yi babban gyara a ma'aikatar sufuri, ya kori daraktoci
Asali: UGC

Rahoton ya alakanto wani majiya na fadin cewa an hade babban sashin hukumar jirgin sama da hukumar DAWS sannan an ba daraktocin biyu, Kyaftin Ayodele Sasegbon da Injiniya Ita-Awak takardun sallama.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Majalisar zartaswa ta fitar da $3.1bn don bunkasa hukumar Kwastam

Har ila yau, an hade hukumar horarwa da hukumar bayar da lasisi inda Kyaftin Bahago E.A ya zama darakta yayinda Kyaftin Abdullahi Sidi ya samu takardar sallama daga aiki.

Gwamnatin tarayya ta yi sauye-sauye makamanci haka a hukumar a watan Fabrairun 2017. Abun ya shafin wasu daraktoci a wancan lokacin.

A baya mun ji cewa, Gwamnatin tarayya ta dage ranar dawo da zirga-zirgan jiragen waje wanda aka shirya yi a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta zuwa ranar 5 ga watan Satumba.

Legit.ng ta rahoto cewa ma’aikatar sufurin jirage ce ta sanar da hakan a ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, a lokacin taron kwamitin fadar Shugaban kasa kan COVID-19, a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar.

Ma’aikatar ta sanar da ci gaban ne a shafinta na twitter, @fmaviationg, inda ta ba ‘yan Najeriya hakuri a kan dagewar da ta yi.

“Da dumi-dumi: Muna danasanin sanar da cewar an dage dawo da zirga-zirgan jiragen sama da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Agusta zuwa ranar 5 ga watan Satumba 2020,”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng