Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara ya koma PDP

Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara ya koma PDP

Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara yayin mulkin tsohon gwamna Abdulaziz Yari, Sanda Danjari, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP mai mulki a jihar.

Danjari, wanda ya bar jam'iyyar APC, ya samu tarbar arziki a ranar Laraba daga wurin Gwamna Bello Matawalle a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.

Kamar yadda yace, yanayin kwazon gwamnan da salon mulkinsa ya ja shi komawa tafiyarsa, jaridar Daily Nigerian ta wallafa.

Ya jinjinawa gwamnan a fannin tsaro da shugabanci nagari, wanda yace hakan suna daga cikin dalilan komawarsa jam'iyyar PDP.

Tsohon kwamishinan ya yi kira ga gwamnan da kada yayi kasa a guiwa wurin samar da tsaro tare da shugabanci nagari a jihar. Ya tabbatar da bada gudumawarsa wurin ganin ci gaban jam'iyyar a jihar.

A jawabinsa, shugaban jam'iyyar PDP na jihar, Ibrahim Mallaha, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Hassan Damri, ya ce za su ci gaba da tabbatar da goyon bayansu ga jam'iyyar.

Mallaha ya ce kofar jam'iyyar PDP a bude take wurin karbar mutanen da za su kara mata daraja tare da cigabanta a fadin jihar.

Matawalle ya bayyana cewa, babu shakka Danjari yana da abubuwan da jihar za ta amfana da su ta fannin ci gaba. Ba jihar kadai ba, hatta jam'iyyar PDP a jihar da kasa baki daya.

Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara ya koma PDP
Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara ya koma PDP. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Shugaba Keita na kasar Mali yana kwance a asibiti, rai a hannun Allah

A wani labari na daban, wani babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Rivers, Cif Ambrose Nwuzi, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

A wani dan kwarya-kwaryan biki da aka yi a garin Afara a karamar hukumar Etche a ranar Lahadi, 30 ga watan Agusta, Gwamna Nyesom Wike ya tarbi tsohon Shugaban na AP da magoya bayansa zuwa PDP, a bisa rahoto daga Rivers News Today.

Ya yake yi wa tsohon Shugaban na APC maraba da zuwa PDP, Gwamna Wike ya yi bayanin cewa sabbi da tsoffin mambobin duk za su samu kula iri guda a jam’iyyar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel